2027: Gwagwarmayar Siyasar Tinubu da Wasu Fitattun Ƴan Takarar Shugaban Kasa
Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027, jam'iyyu daban-daban sun bayyana mutanen da za su yi masu takarar shugaban kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Zuwa yanzu, jam'iyyun siyasa akalla 15 ne suka fitar da wadanda za su yi masu takarar shugaban kasa a babban zaben 2027.
Daga cikin wadannan 'yan takara, akwai wadanda suka sha fito wa neman kujerar a baya ba tare da sun samu nasara ba.

Source: Facebook
Sannan akwai wadanda wannan shi ne karon farko da suke neman takara a karkashin jam'iyyun siyasa daban-daban.
Legit ta tattaro fitattu daga cikin 'yan siyasa da ke neman kujerar da Bola Tinubu ke kai a zaben 2027 da takaitaccen bayani game da siyasarsu a Najeriya.

Kara karanta wannan
Lokuta 6 da Atiku ya nemi samun kujerar shugaban kasa da yadda takarar ta kasance
Fitattun 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya
Wasu daga cikin wadanda ke neman takarar shugaban kasa a babban zaben Najeriya sun hada da shugana da ke kan mulki da wasu fitattun 'yan siyasa da suka yi suna a kasar.
Ga jerin fitattun 'yan takarar da aka bayyana za su yi takara tare da takaitaccen tarihinsu kamar haka:
1. Bola Ahmed Tinubu
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kuma yin takara a babban zabe mai zuwa.
Tinubu ya tsunduma a siyasa a shekarar 1992 inda aka zaɓe shi a matsayin Sanatan Lagos ta Yamma a ƙarƙashin jam'iyyar SDP, INda ya shugabanci wasu manyan kwamitocin majalisar dattawa.

Source: Getty Images
Bayan rikicin siyasar da ya biyo bayan soke zaɓen 1993 na MKO Abiola, Tinubu ya tsere ƙasashen waje a lokacin mulkin soja na Sani Abacha, kafin ya dawo Najeriya bayan rasuwarsa a 1998.
Bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya, Tinubu ya zama gwamnan Legas a 1999 sannan ya sake lashe zaɓe a 2003.
Ana yi masa lakabi da "Jagaba" a tsakanin magoya bayansa. Yana neman wa'adi na biyu tare da alkawarin kara inganta tsaro, bunkasa ababen more rayuwa da kuma magance kalubalen tattalin arziki.
2. Atiku Abubakar
Channels TV ta ruwaito cewa Alhaji Atiku Abubakar Atiku, tsohon 'dan takarar shugaban Najeriya ya samu tikitin takarar shugaban kasa a ADC.
Sai dai akwai damuwa a jam'iyyar ganin cewa ya samu tikitin takara ne a tsagi daya, wanda Sanata David Mark ke jagoranta.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fara fafutukar neman kujerar shugaban kasa tun shekarar 1992/1993, kuma ya ci gaba da yin takara har zuwa yau.
A 1992/1993, Atiku ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP, amma ya sha kaye a zaben fitar da gwani a hannun Moshood Kashimawo Olawale Abiola.
A 2007, ya sake tsayawa takara karkashin jam’iyyar AC, inda ya zo na uku a babban zaben da Umaru Musa Yar’Adua ya lashe.
A 2011, ya nemi tikitin jam’iyyar PDP amma ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan a zaben fitar gwani. A shekarar 2015 ma ya tsaya takara, inda Muhammadu Buhari ya doke shi a zaben.
A 2019, ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP amma ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.
A 2023 kuma, ya sake tsayawa takara a PDP, inda Bola Ahmed Tinubu ya doke shi, inda Yanzu kuma ya ke takarar a inuwar ADC.
3. Peter Obi
Premium Times ta wallafa cewa Peter Obi ya samu tikitin jam'iyyar NDC bayan ficewarsa daga LP da ADC a baya-bayan nan a kokarinsa na samun takarar.
Siyasar Obi ta fara armashi a shekarar 2003 inda aka zabe shi gwamnan jihar Anambra. Ya ci gaba da jagorantar jihar bayan ya yi nasarar kare kujerarsa ta hanyar shari’o’i da dama.
A watan Nuwamban 2006, an tsige shi daga mukaminsa, amma ya kalubalanci matakin a kotu. Daga bisani, kotu ta mayar da shi kan kujerarsa a watan Fabrairun 2007.
A shekarar 2007, ya sake lashe zaben gwamna kuma ya ci gaba da mulkin jihar Anambra har zuwa shekarar 2014.

Source: Facebook
Bayan ya bar mulki a 2014, Obi ya ci gaba da taka rawa a siyasar Najeriya. A shekarar 2019, jam’iyyar PDP ta zabe shi a matsayin abokin takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku Abubakar.
Sai dai sun sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC. A shekarar 2023, Peter Obi ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP inda ya samu kuri'u miliyan 6.1
A yanzu kuma yana takara a inuwar jam'iyyar NDC tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso inda suke neman hade kan Arewa da Kudu domin a zabe su a ba ban zaben.
4. Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya samu tikitin wani bangaren PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki.
Goodluck Jonathan ya fara harkokin siyasa ne a ƙarshen shekarun 1990 lokacin da ya shiga jam’iyyar PDP. A shekarar 1999, an zaɓe shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bayelsa. Ya riƙe wannan muƙami har zuwa shekarar 2005, lokacin da ya zama gwamna bayan an tuhumi gwamnan jihar da cin hanci tare da tsige shi daga muƙami. A shekarar 2007, jam’iyyar PDP ta zaɓe shi a matsayin abokin takarar mataimakin shugaban ƙasa na Umaru Musa Yar’Adua. Sun lashe zaɓen shugaban ƙasa kuma aka rantsar da su a watan Mayun 2007.

Source: Twitter
A farkon shekarar 2010, rashin lafiyar Yar’Adua da doguwar jinyarsa a ƙasashen waje ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.
A ranar 9 ga Fabrairun 2010, Majalisar Tarayya ta bai wa Jonathan cikakken ikon gudanar da mulki a matsayin shugaban ƙasa na riƙo.
Bayan dawowar Yar’Adua Najeriya a ranar 24 ga Fabrairun 2010, Jonathan ya ci gaba da zama shugaban ƙasa na riƙo yayin da shugaban ke jinya.
A watan Mayun 2010, Umaru Musa Yar’Adua ya rasu, kuma washegari aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban ƙasar Najeriya.
A watan Satumban 2010, Jonathan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2011.Daga bisani, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen fitar da gwani.
Muhammadu Buhari ya doke shi a 2015, kuma kafin a gama tattara kuri'u ya sallama, ya mika mulki salin-alin ba tare da wani tashin hankali ba. Ya samu kuri'a 12,853,162 a lokacin.
Har yanzu bai yi cikakken bayani a bainar jama'a kan batun tsayar da shi takara ba domin makusantansa sun ce tsagin PDP ne kawai ke kidansa yana rawarsa, kamar yada Daily Post ta wallafa.
5. Seyi Makinde
Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Seyi Makinde, wanda shi ne Gwamnan jihar Oyo na wannan lokaci zai yi takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APM.
Tun bayan nasararsa a zaben 2019 a Oyo, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun gwamnoni a Najeriya, yana mai da hankali kan ci gaban jihar da inganta rayuwar al’umma.
Sai dai duk da hadin gwiwa da jam'iyyar APM, rahotanni sun ce har yanzu bai sanar da ficewa daga PDP ba.

Source: Twitter
Daily post ta wallafa cewa tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP, Umar Sani, Sowore ya yi gaban kansa ne wajen hadin gwiwar, kuma manyan PDP za su bayyana dauki mataki nan gaba.
6. Omoyele Sowore (AAC)
Voice of Nigeria ta kawo labarin cewa cewa Omoyele Sowore shi ne dan takarar jam'iyyar AAC a zabe mai zuwa.
Sowore dan jarida ne kuma wanda ya kafa Sahara Reporters da kuma jam'iyyar AAC, kuma ya dade yana kiran kansa a matsayin 'dan gwagwarmaya.
Wannan ne karo na uku a jere da zai tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar da ya kafa.

Kara karanta wannan
Jerin matan Arewa 4 da jam'iyyar APC ta tsaida takarar Majalisar wakilai a zaben 2027
A zaben 2019 ya samu kuri'u 33,953 inda ya zo na biyar, yayin da a zaben 2023 ya samu kuri'u 14,608.

Source: Facebook
Sauran masu neman takarar shugaban kasa
Bayan wadannan fitattun 'yan takara, akwai Adewole Adebayo da ya samu tikitin SDP, da Abimbola Akeem Atanda kuma a SDP.
Dumebi Kachikwu ya samu takara a tsagin ADC, yayin da Chris Uba ya samu tikitin wani bangaren ADC karkashin shugabancin Bala Gombe.
Tsohon hadimin Atiku, Aliyu Bin Abbas ya samu tikitin ADP, Chibuzo Okereke ya samu tikitin LP, Gbenga Olawepo-Hashim na jam'iyyar AP, Donald Duke ya samu na PRP yayin da Sandy Onor a tsagin Wike na PDP.
Birtaniya ta magantu kan zaben Najeriya
A baya, mun wallafa cewa kasar Birtaniya ta yi magana musamman game da zaben shugaban kasa a shekarar 2027 da ake tunkara a Najeriya da ake ganin zai yi zafi.
Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Gill Lever, ta ce gwamnatin Birtaniya ba ta da dan takara da ta fi so a babban zaben 2027 da ke tafe a Najeriya, sa ido ne kawai na ta
Ta kara da cewa gwamnatin Birtaniya ba za ta tsoma baki a zabukan Najeriya ba, za ta goyi bayan sahihanci da zaman lafiya a lokacin da jama'a ke kad kuri'a don zaɓen shugabansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




