Atiku Ya Lallasa Yan Takara 2, Ya Samu Nasara a Zaben Fitar da Gwanin ADC a Sakkwato

Atiku Ya Lallasa Yan Takara 2, Ya Samu Nasara a Zaben Fitar da Gwanin ADC a Sakkwato

  • Sakamakon fitar da gwanin jam'iyyar ADC na takarar shugaban kasa da aka gudanar yau Litinin ya fara fitowa daga jihohin Najeriya
  • Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 68,823 inda ya kayar da sauran ‘yan takarar da suka fafata, Rotima Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen a Sokoto
  • Daga cikin manyan kusoshin da suka halarci wurin tattara sakamakon akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu rinjaye a zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC da aka gudanar a jihar Sakkwato.

Idan baku manta ba, jam'iyyar adawa ta ADC ta gudanar da zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a yau Litinin, 25 ga watan Mayu, 2026 a fadin jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan ADC za su san makomarsu game da takarar shugaban kasa

Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a kan layi a wurin zaben fitar da gwanin ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

ADC ta sanar da sakamako a Sakkwato

Daily Trust ta ruwaito cewa a sakamakon da aka bayyana a jihar Sakkwato, ya nuna cewa Atiku ya kayar da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen a jihar Sakkwato, Aminu Abubakar, ne ya sanar da sakamakon a ranar Litinin, yana mai cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana.

Ya ce Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 68,823 inda ya kayar da sauran ‘yan takarar da suka fafata a zaɓen.

Atiku ya kayar da Amaechi a Sakkwato

Bisa ga sakamakon da aka bayyana, tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya samu ƙuri’u 292, yayin da Muhammad Hayatuddeen ya samu ƙuri’u 319.

Malamin jami’ar ya ce jimillar ƙuri’u 69,434 aka kaɗa a zaɓen fitar daa gwanin jam'iyyar hadaka ta ADC, kamat yadda Leadership ta kawo.

“Saboda haka ina ayyana Alhaji Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ya samu mafi yawan ƙuri’u a jihar Sokoto,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Ba dan koyo ba"; Atiku ya gano dan takarar da ya cancanci tutar ADC don karawa da Tinubu 2027

An sanar da sakamakon ne a gaban jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), jami’an tsaro da shugabannin jam’iyya.

Manyan jiga-jigan ADC sun halarci wurin

Daga cikin manyan kusoshin da suka halarci wurin tattara sakamakon akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da ɗan takarar gwamna na ADC a jihar, Mannir Dan Iya.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a taron kaddamar da hadaka a jam'iyyar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Haka zalika, ɗan takarar Sanatan Sokoto ta Kudu, Faruk Malami Yabo, da shugaban jam’iyyar ADC na jihar, Abdullahi Maigwandu da sauransu sun halarci wurin.

Tun da farko ADC a jihar Sakkwato ta ayyana Atiku a matsayin ɗan takara guda tilo da take goyon baya kafin gudanar da zaɓen fitar da gwanin.

Atiku ya yi magana kan takarar ADC

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana cewa dole ne jam'iyyar ADC ta tsayar da ɗan takara da ya cancanta da kuma gogewa, wanda zai iya warware matsalolin Najeriya.

Atiku ya ce zaɓin da ke gaban wakilan ADC ya wuce batun siyasa kawai, inda ya bayyana shi a matsayin wani babban nauyi na tarihi.

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, an kafa ADC ne a kan ginshiƙai na gaskiya, riƙon amana, haɗa kai, da kuma sabunta tsarin demokraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262