Zaben Bayelsa: APC da Oshiomhole sun yabawa karamcin Goodluck Jonathan

Zaben Bayelsa: APC da Oshiomhole sun yabawa karamcin Goodluck Jonathan

Mun samu labari cewa jam’iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya ta yaba da yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi zaben jihar Bayelsa da aka ayi a makon jiya.

APC ta bayyana cewa Goodluck Jonathan ya ji dadin yadda zaben ya kasance duk da ‘dan takarar jam’iyyar hamayya a jihar, David Lyon ne ya yi nasara a kan ‘Dan takarar PDP, Diri Douye.

Shugaban gwamnonin APC a Najeriya, Sanata Atiku Bagudu ya yi magana a kan zaben, bayan da APC ta gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘dan takarar na su a fadar Aso Villa.

Atiku Bagudu ya ke cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi murna da yadda zaben ya kasance. Ya ce: “Kwananmu uku a jihar Bayelsa, amma ba mu ga an kona da ko da tayar mota ba.”

“Ba mu ga mutane su na gudu ba, ba mu ji harbin bindiga a ko ina ba. Duk inda mu ka wuce tun jiya (Ranar Lahadi), murna kawai ake ta faman yi, wannan ya nuna karbuwar ‘dan takararmu.”

KU KARANTA: Ana kishin-kishin din dakatar da Jonathan daga Jam'iyyar PDP

Gwamnan Kebbi ya kara da: “Haka zalika duk da Bayelsa Garin tsohon shugaban kasa Jonathan, kuma wata jam’iyya ta dabam ta karbe mulki, abin da mu ke gani shi ne ya amince da zaben.”

A cewar shugaban gwamnonin na jam’iyyar APC, abin da su ke jin labari kuma su ka gani a zahiri daga Jonathan shi ne ya karbi nasarar APC da hannu biyu wanda ya nuna sahihancin zaben jihar.

Shugaban jam’iyyar ta APC, Adams Oshiomhole wanda ya gabatar da gwamnan da za a rantsar a Ranar masoya ta Duniya ya ce wannan ne karon farko da aka yi zaben gaskiya a Bayelsa tun 1999.

Oshomhole ya kuma yabawa Goodluck Jonathan wanda ya ce ya nuna saukin kansa da kirki da jajircewa wajen karbar Jagororin APC. Sannan Oshiomhole ya gode da kokarin Timipreye Sylva.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel