Sarkin Ringim Ya Yi Babban Rashi, Allah Ya Karbi Ran Matarsa Mai Shekaru 83
- Matar Sarkin Ringim, Hajiya Aisha Sayyadi Mahmud, ta rasu tana da shekaru 83 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a Ringim
- Rasuwar Hajiya Aisha ta jefa Masarautar Ringim cikin jimami, inda al’umma suka bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai kaunar jama’a
- Gwamna Umar Namadi ya halarci jana’izarta, tare da yi mata addu’ar samun rahamar Allah, sannan ya roƙi iyalanta haƙurin babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ringim, Jigawa - Matar Sarkin Ringim, Hajiya Aisha Sayyadi Mahmud, ta rasu tana da shekaru 83 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a garin Ringim.
Hajiya Aisha ta rasu ranar Laraba, 12 ga Agusta 2026, lamarin da ya jefa al’ummar Masarautar Ringim cikin jimami da alhini.

Source: Original
Mutane da dama sun bayyana marigayiyar a matsayin uwa ga al’umma, saboda yadda ta kasance mai kusanci da taimakon jama’a, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan
Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita
Marigayiyar ta bar mijinta, Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahmud, da ’ya’yanta, ciki har da Chiroman Ringim Alhaji Usman Sayyadi da sauran ’yan uwa.
Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya halarci jana’izar marigayiyar da aka gudanar a Ringim, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata.
Gwamnan ya roƙi Allah Ya jiƙanta da rahama, Ya sanya ta a Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalanta haƙurin wannan babban rashi.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga Sarkin Ringim, Masarautar Ringim da ɗaukacin al’ummar garin, yana addu’ar Allah Ya ba su ƙarfin jure rashi.
Al’ummar Ringim sun ci gaba da bayyana alhininsu kan rasuwar Hajiya Aisha, tare da yi mata addu’o’in neman rahamar Allah da gafara.
Ajiyan Yara, daya daga cikin hadiman masarautar ta tabbatar da cewa an gudanar da jana'izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Ya bayyana haka ne a shafin Facebook, inda ya ce manyan mutane cikin har da Gwamna Umar Namadi sun samu halartar jana'izar.
Ya ce:
"An gudanar da jana’izar matar Mai Martaba Sarkin Ringim, wadda kuma ita ce mahaifiya ga Chiroman Ringim, babban ɗan Majalisar Sarki, Alh. Usman Sayyadi Ringim.
Jana’izar ta samu halartar Mai Girma Gwamna da sauran manyan baki, sarakuna, malamai da al’umma daga sassa daban-daban.
Muna roƙon Allah Ya jiƙan marigayiya, Ya gafarta mata, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, sannan Ya bai wa iyalai da masarautar Ringim haƙurin rashinta. Amin."
An yi rashin malamin Musulunci a Maiduguri
A baya, mun ba ku labarin cewa wani fitaccen malamin addinin Musulunci ya rasu a Maiduguri ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026 da muke ciki.
Wani matashi, Ibn Maigana ya sanar da rasuwar malamin, yana bayyana shi a matsayin mashahurin malami da ya ilmantar tare da tasiri ga al'ummar Bolori.
Bayan rasuwarsa, jama'a sun ci gaba da yi masa addu'a, yayin da aka tuna gudummawarsa ga addini, ilimi da tarbiyyar al'umma a Maiduguri da kewaye.
Asali: Legit.ng
