ADC Ta Ji Kamshin Hadakar 'Yan Adawa, Ana Son Tsayar da Dan Takara Ya Tunkari Tinubu

ADC Ta Ji Kamshin Hadakar 'Yan Adawa, Ana Son Tsayar da Dan Takara Ya Tunkari Tinubu

  • ADC ta ce har yanzu akwai yiwuwar jam’iyyun adawa su hada a fitar da dan takara guda wanda zai fafata da shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu
  • Jam’iyyar ta ce hadin kan ‘yan adawa wanda zai tara karfinsu waje daya zai kara musu damar samun nasara a kan APC a zaben 2027
  • Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar za ta kare kuri’un magoya bayanta da hana magudin zabe ta hanyar doka a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam’iyyar ADC ta ce har yanzu ba ta yi watsi da yiwuwar kafa kawancen jam’iyyun adawa gabanin babban zaben 2027 ba, duk da ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga tsarin kawancen.

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita

Kakakin jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana haka yayin wata hira, inda ya ce ADC ta yi imanin cewa ‘yan adawa za su fi samun damar kayar da jam’iyyar APC idan suka hada karfi wuri guda.

ADC ta bullo da sabuwar dabara don a kawar da Tinubu
Alamar jam'iyyar ADC, Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: ADC Coalition 2027/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

A hirar da ta kebanta da Nigerian Tribune, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa wannan kawancen zai zama babban makamin yan adawa ga gwamnati mai ci.

ADC ta hango nasarar Atiku

Politics Nigeria ta kawo labarin cewa ADC ta fara aikin hada kan ‘yan adawa ne saboda imanin cewa aiki tare zai kara masu karfi a zaben 2027.

Sai dai ya jaddada cewa, ko da ba a samu cikakken kawance ba, ADC na da yakinin samun nasara saboda ta ce tana da goyon bayan al’ummar Najeriya.

A cewarsa, jam’iyyar ta yi imanin cewa matsalolin rashin tsaro, yunwa da wahalhalun tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta za su iya sauya sakamakon zaben 2027.

ADC za ta kare kuri'unta

Bolaji Abdullahi ya kuma bayyana cewa ADC za ta gudanar da yakin neman zabe ne cikin bin doka, tare da daukar matakan kare kuri’un da magoya bayanta suka kada.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

ADC ta ce Atiku zai ci zabe ko ba hadakar adawa
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto; Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Ya ce jam’iyyar ba za ta tsaya kawai wajen wayar da kan jama’a su kada kuri’a ba, za ta tabbatar da cewa an kare kuri’unsu.

A kalaman Bolaji Abdullahi:

"Ba wai za mu wayar da kai a zo a kada kuria'a ba ne, za mu tabbatar mun kare kuri'ar da aka kada mana."

Ya kuma zargi gwamnatin APC da kokarin amfani da wasu hanyoyi wajen raunana ‘yan adawa, ciki har da batun tsare tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Tsohon Minista ya maka ADC a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 29 ga Satumba 2026 domin sauraron karar da Mohammed Hassan Abdullahi ya shigar kan zaben fidda gwani na ADC a Nasarawa.

Kungiyar yakin neman zaben tsohon ministan ta ce ta yi watsi da ayyana Nuhu Angbazo a matsayin wanda ya lashe zaben inda ta sha alwashin ci gaba da shari’ar har zuwa kotun karshe idan hakan ya zama dole.

Ya bayyana shari’ar a matsayin “ta musamman”, yana zargin cewa jam’iyyar ta soke sakamakon wata karamar hukuma baki daya inda Abdullahi ya samu fiye da kuri’u 10,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng