'Lokaci Ya Wuce da za a Zabi Mutum saboda Kwankwaso': 'Dan Majalisar Kano
- Dan majalisar Kano Sulaiman Mukhari Ishaq Madobi ya ce komawarsu APC ya samo asali ne daga muradin yin abin da ya dace wa jama’a
- Ya shaidawa Legit yadda aka juyar da ra'ayin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi yunkurin komawa APC kafin a raba shi da Gwamna
- Hon Mukhari ya ce lokaci ya wuce da ake zabar mutum kawai saboda Jagora, yana mai cewa aikin da aka yi wa jama’a shi ne ya kamata ya zama abin dubawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar Madobi, Hon. Sulaiman Mukhtari Ishaq, ya bayyana cewa sauyin sheka da ya yi zuwa jam’iyyar APC tare da wasu ‘yan siyasa na jihar ya samo asali ne daga muradin yi wa jama’a abin da ya dace.
A wata hira da Legit, Hon. Mukhtari ya bayyana cewa an samu sabanin fahimta ne bayan gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da tayin komawa APC da jam’iyyar ta dade tana yi.

Source: Facebook
Dan majalisar, wanda shi ne dan takarar majalisar tarayya na APC mai wakiltar mazabar Kura/Madobi/Garun Malam, ya kuma ce yana da hujjojin da ke nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taba nuna aniyarsa ta komawa APC.
Yadda aka samu sabani kan komawa APC
Da yake bayani kan yadda lamarin ya faru, Dan majalisar ya ce akwai wasu mutane da ke kusa da Kwankwaso da suka nuna rashin amincewa da yiwuwar rabuwa tsakanin jagoran da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A kalamansa:
“Domin ni ina fada da hujja cewa jagoran APC yake so ya yi, amma akwai wasu mutane da suke kewaye da shi wadanda su kuma babbar matsalarsu shi ne suna ganin ya ya mai girma gwamna zai rabu da jagora, kuma suka yi nasara.”

Source: Facebook
Ya kara da cewa bayan haka ne suka yanke shawarar komawa gefe guda domin tantance abin da ya dace wanda zai yi masu da mutanen Kano kyau.
A cewarsa, wannan ne dalilin da ya sa suka bi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC, ba wai don kiyayya, gaba ko kyashi ba.
An wuce lokacin zabar mutum saboda Jagora
Hon. Sulaiman Mukhtari Ishaq Madobi ya ce yana alfahari da yadda aka san shi a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisar da ke kokarin kai matsalolin al’ummarsu gaban majalisa.
Ya ce abin da ya kamata a duba shi ne aikin da dan siyasa ya yi wa jama’a da irin ci gaban da ya kawo, ba wai kawai kasancewarsa mabiyin wani jagora ba.
A cewarsa:
“Muna so a zabi mai girma gwamna saboda aikin alherinsa da aka gani, mu ma muna so a zabe mu saboda abubuwan da muka iya kwatantawa suka gani.”
“Lokaci ya wuce da za a ce wai yau sai dai a yi ta zaben mutum saboda jagora.”
Dan majalisar ya ce wasu mutane na samun abin da ya kira “romo na jagora”, wanda ke sa su yi imanin cewa za su iya samun mukami ko da kuwa ba su yi wani abin kirki ga al’umma ba.
Sai dai Mukhari ya ce Kwankwaso mutum ne mai kirki, amma an samu sabanin fahimta ne wanda ya haifar da rarrabuwar tafiyarsu a wannan karon.
Gwamnan Kano ya waiwayi jami'o'i
A baya, kun samu labarin cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya waiwayi wasu daga cikin jami'o'in da ke jihar da karin albashi inda aka fitar masu da sabon tsari.
Gwamnatin jihar za ta kashe sama da N391m duk wata wajen biyan sabon tsarin albashin ma’aikatan jami’o’in biyu zuwa irin na Gwamnatin Tarayya saboda inganta rayuwarsu.
Bayanin wannan sabon tsari na dauke a cikin wata sanarwa da Darakta Janar kan harkokin yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin 10 ga watan Agusta, 2026.
Asali: Legit.ng


