Bayan Rahoton Legit Hausa, Gwamna Ya Gana da Matashin da Ya Daina Tallata Tinubu

Bayan Rahoton Legit Hausa, Gwamna Ya Gana da Matashin da Ya Daina Tallata Tinubu

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya gana da wani matashi domin ƙarfafa masa gwiwa wajen ci gaba da wayar da kan jama’a
  • Adam Fakai ya dakatar da tallata ayyukan Tinubu bayan ya ce ya shafe shekaru biyu yana amfani da kuɗinsa, ba tare da samun tallafi ba
  • Bayan ganawa da gwamnan, Fakai ya samu sabon ƙwarin gwiwa na ci gaba da wayar da kan jama’a kan ayyukan gwamnatin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya gana da wani matashi da ya watsar da tallar Bola Tinubu saboda rashin kulawa da shi.

Matashin mai suna Adam Fakai ya samu kyautar mota daga gwamnan domin ci gaba da wayar da kan jama’a kan manufofin gwamnatin Tinubu.

Gwamna ya ba matashi mota da ya watsar da Tinubu
Adamu Yahaya, wanda aka fi sani da Adam Fakai da ya dakatar da tallata gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: @officialABAT, @Adamfakai.
Source: Twitter

Fakai shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa inda ya ce ya dauki lokaci mai tsawo yana tallar Tinubu ba tare da samun komai ba.

Kara karanta wannan

Duka bayanan da suka fito daga juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Tinubu

Dalilin Fakai na dena tallata Bola Tinubu

Matakin ya biyo bayan sanarwar Fakai cewa zai dakatar da tallata ayyukan gwamnatin Tinubu saboda rashin kulawa da tallafi daga jami’an gwamnati.

Fakai ya ce ya shafe kusan shekaru biyu yana amfani da lokacinsa da kuɗinsa wajen wayar da kan jama’a kan ayyukan gwamnati.

Bayan labarin ya yaɗu wanda Legit Hausa ta wallafa, Gwamna Nasir Idris ya gayyaci Fakai zuwa gidan gwamnati domin tattauna dalilan da suka sa ya dakatar da aikin.

Matashi ya samu kyautar mota daga gwamnan Kebbi
Matashi Adam Fakai da ya bar tallata Bola Tinubu saboda rashin kulawa. Hoto: @Adamfakai.
Source: Facebook

Gwamna Idris ya karfafawa Fakai guiwa

A yayin ganawar, gwamnan ya ƙarfafa masa gwiwa tare da bayyana muhimmancin aikin da yake yi wajen isar da bayanai ga jama’a

Ya jaddada cewa wayar da kan jama’a ta kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa na taimakawa wajen fahimtar manufofi da ayyukan gwamnati.

A cewar Fakai, gwamnan ya bayyana irin ƙoƙarin da Shugaba Bola Tinubu ke yi wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya da bunƙasa ƙasar.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Gwamnan ya kuma ce matasa masu kishin ci gaban ƙasa suna da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma da yada sahihan bayanai.

Domin ƙara masa ƙwarin gwiwa, Nasir Idris ya ba Fakai mota domin sauƙaƙa masa zirga-zirgar tattara bayanai da tallata ayyukan gwamnatin tarayya da Kebbi.

Bayan samun wannan tallafi, Fakai ya bayyana cewa ya samu sabon ƙarfin gwiwa na ci gaba da aikin wayar da kan jama’a.

Matakin ya ƙara nuna goyon bayan Gwamna Nasir Idris ga gwamnatin Bola Tinubu da kuma matasan da ke tallata manufofin gwamnatin APC.

Masoyin Tinubu ya yaba wa uwar dakinsa, Oluremi

A wani labarin, an ji cewa wani masoyin Bola Tinubu ya yaba wa Sanata Oluremi Tinubu kan shirinta na ƙarfafa mata a Najeriya.

Ya yi amfani da labarin Asabe mai sayar da kosai da koko a Abuja, wadda ta gina gidaje daga ribar kasuwancinta.

Matashin wanda dan a mutun APC ne ya buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su tallafa wa mata da jari, horo da kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.