Pantami da Masu Neman Gwamna da Suka Sauya Sheka bayan Rasa Tikiti a APC
'Yan siyasa da dama sun sauya sheka bayan kammala zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC mai mulki da wasu jam'iyyun adawa suka yi gabanin zaben 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Zaben fitar da gwani da jam'iyyun siyasa suka yi gabanin zaben 2027 ya bayar baya da kura a jihohi da dama a Najeriya.
'Yan siyasa daga jam'iyyu da dama sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin takara, inda wasu suka ce ba a masu adalci ba.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun kawo muku jerin 'yan siyasa da suka da suka fita daga jam'iyyar APC bayan rasa tikirin takarar gwamna na 2027.
1. Sheikh Isa Ali Pantami
Tsohon mnistan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya koma PDP daga APC tare da samun tikitin takarar gwamnan jam’iyyar.
Ya samu tikitin ne ta hanyar amincewa da murya a zaɓen fitar gwani da aka gudanar, an ayyana shi a matsayin ɗan takara guda ɗaya ta bakin shugaban kwamitin zaɓen PDP, Hon. Gregory Yenlong.
Da yake magana jim kaɗan bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Pantami ya ce ya nemi takarar ne domin yi wa al’ummar jihar hidima.
Daily Trust ta wallafa cewa Pantami ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a shekarar 2027, zai gudanar da mulki cikin adalci da gaskiya.

Source: Facebook
Tun da farko, Pantami ya nuna rashin amincewa da tsarin da ya haifar da fitowar Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha na APC.
Ya bayyana cewa yana son a gudanar da zaɓen fidda gwani, amma ya janye daga takarar a jajibirin zaɓen, yana zargin rashin gaskiya
2. IGP Mohammed Adamu
Tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya yi murabus daga jam’iyyar APC, yana mai cewa yadda aka gudanar da zaɓen fitar gwani na gwamnan jihar Nasarawa ya saɓa wa ƙa’idojin adalci da dimokuraɗiyya.
A cikin wata sanarwa, shugaban hulɗa da jama'a ta kungiyar yaƙin neman zaɓen shi, Isa Nathaniel ya ce tsohon shugaban ’yan sandan ya koma jam’iyyar SDP a hukumance.
The Nation ta rahoto ya ce:
“Bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, wakilan zaɓe, magoya baya da jajirtattun ’yan jam’iyya a faɗin jihar Nasarawa, Mohammed Adamu da tafiyarsa ta siyasa sun yi murabus daga jam’iyyar APC a hukumance tare da shiga jam’iyyar SDP,”

Source: Twitter
Ya kara da cewa:
“An yanke wannan shawara ne bayan abin kunyar da ya faru a zaɓen fitar da gwani na gwamnan APC da aka gudanar a ranar 21 ga Mayu, 2026, wanda aka yi ƙoƙarin nuna kamar sahihin zaɓe ne.”
3. Sanata Shehu Buba
Sanatan da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba, kuma tsohon ɗan takarar gwamna a APC, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai zargin rashin bin tsarin dimokuraɗiyya.
Arise News ta wallafa cewa Sanata Shehu Buba da ya nemi tikitin takarar gwamna a APC, ya janye daga takarar ne kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen fitar gwani.
Yayin da yake sanar da sauya sheƙarsa daga APC a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da sadarwa, Sabo Mohammed, ya ce yanzu ya koma jam’iyyar PRP.

Source: Facebook
Sanatan ya ƙara da cewa nuna wariya ga haƙiƙanin mambobin jam’iyya da kuma ƙara yin watsi da ra’ayoyi da muradun magoya bayan jam’iyyar a matakin ƙasa a APC, na daga cikin dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar.
4. Kunle Olatunji
Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan Jihar Oyo a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Mista Kunle Olatunji, ya fice daga jam’iyyar bayan rasa tikiti.
Rahotanni sun nuna cewa Olatunji ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da jaridar Daily Post a makon da ya wuce.
Olatunji, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Ona Ara da ke Ibadan, ya ce ya koma jam’iyyar ADP domin cimma burinsa na siyasa a 2027.
Gargadin Shettima kan sauya sheka
A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi nasiha ga 'yan jam'iyyar APC gabanin zaben fitar da gwani.
Shettima ya bukaci dukkan wadanda suka fadi a zaben fitar da gwani da su zauna a cikin jam'iyyar ba tare da sun koma wata tafiyar siyasa ba.
Ya bayyana cewa dama dole ne a samu wanda ya fadi idan aka yi zabe, lamarin da ya ce yana da kyau ya sanya kowa ya shirya karbar kaddara idan ya sha kaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


