Ana cikin Sukar Kalaman Shekh Jingir, ADC Ta Tsaida Tikitin Takarar Musulmi da Musulmi a 2027
- Jam'iyyar ADC ta tsayar da Hon Mamman Musa daga Bosso a matsayin dan takarar mataimakin gwamna a jihar Neja
- Matakin ya zo ne duk da kiran wasu matasan Kiristoci na kauce wa zaɓar ’yan takarar da za su hada tikitin Musulmi da Musulmi
- Kpautagi ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan tsaro, noma, kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Sabanin abin da wasu matasan Kiristoci a jihar Neja ke tsammani, ɗan takarar gwamnan jam’iyyar ADC, Alhaji Mohammed Kpautagi, ya zaɓi Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.
Kpautagi ya bayyana tsohon Kwamishinan Ayyuka, Alhaji Mamman Musa daga Bosso, a matsayin ɗan takararsa na mataimakin gwamna.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa matakin ya zo ne bayan wasu matasan Kiristoci sun yi barazanar kin zaɓar duk wani ɗan takarar gwamna da zai fito da tikitin Musulmi da Musulmi.
Matasan Kiristoci ba su yi tsammani ba
Wasu matasan Kiristoci sun nuna adawa da tikitin Musulmi da Musulmi musamman bayan gwamnan Neja kuma ɗan takarar APC, Mohammed Umaru Bago, ya zaɓi Musulmi a matsayin abokin takararsa.
Saboda haka, akwai tsammanin cewa ADC za ta zaɓi Kirista a matsayin mataimakin Kpautagi domin samar da tikitin da ya bambanta da na APC.
Sai dai hakan bai ssmu ba, bayan Kpautagi ya bayyana Alhaji Mamman Musa, wanda shi ma Musulmi ne, a matsayin abokin takararsa.
Kpautagi ya kare zabinsa
Da yake bayyana dalilin zaɓar Mamman Musa, Kpautagi ya ce ya yi imanin cewa matashin ya dace da aikin kuma zai iya haɗa matasa cikin harkokin gwamnati.
Ya kuma nuna kyakkyawan fata cewa ADC za ta iya kayar da gwamnatin Mohammed Bago a zaɓen 2027 saboda tana da goyon bayan al’ummar jihar.
Kpautagi ya ce:
“Za mu gudanar da kamfen ba tare da zage-zage ko ɓata sunan mutane ba. Kamfen ɗinmu zai kasance kan batutuwan da suka shafi al’umma.”
Ya yi alkawarin tabbatar da tsaro
Kpautagi ya ce ɗaya daga cikin muhimman manufofin ADC shi ne tabbatar da tsaro, yana mai cewa hakan na cikin alkawuran da jam’iyyar ta ɗauka.
Ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta tallafa wa ’yan kasuwa, manoma da matasa.

Source: Facebook
Ya ce za ta mayar da hankali wajen dawo da masana’antu tare da samar da yanayin da zai ba ƙananan sana’o’i damar bunƙasa, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.
ADC na fatan hadakar yan adawa a 2027
A wani labarin, kun ji cewa ADC ta ce har yanzu akwai yiwuwar jam’iyyun adawa su hadu a fitar da dan takara guda wanda zai fafata da shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu.
Kakakin jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana haka yayin wata hira, inda ya ce ADC ta yi imanin cewa ‘yan adawa za su fi samun damar kayar da jam’iyyar APC idan suka hada karfi wuri guda.
Asali: Legit.ng

