Hashim: Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Yadda Zai Raguzo da Farashin Dala Idan Ya Ci Zabe
- Dan takarar shugaban kasa Gbenga Olawepo-Hashim ya yi alkawarin kawo sauyi daga matakin da Najeriya ke ciki a ƙarƙashin Bola Tinubu
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa da aka jefa jama'a
- Ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da bin doka tare da shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana domin a farfaɗo da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan kasuwar makamashi na duniya, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi alkawarin mayar daukaka darajar Naira da zarar ya samu mulki.
Ya yi alkawarin cewa zai daga darajar Naira zuwa tsakanin N500 da N525 kan kowace Dala ta Amurka idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan
Tsagin PDP na cikin barazanar rasa Jonathan a matsayin 'dan takarar shugaban kasa

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Hashim ya bayyana hakan ne yayin wani babban taron magoya bayan jam'iyyar AP da aka gudanar a Dawaki da ke Abuja ranar Alhamis 4 ga wanan Mayu, 2026.
Dubunnan magoya baya da sauran ƴan jam'iyya ne suka hallara domin nuna goyon bayansu ga burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Hashim na shirin gyara Najeriya
The Nation ta kawo labarin cewa da yake jawabi ga mahalarta taron, Hashim ya gode wa magoya bayansa bisa juriyarsu da kuma biyayyarsu ga jam'iyyar duk da ƙalubalen da suka fuskanta a lokacin zaben fitar da gwani.
Sai dai ya yi amfani da damar wajen caccakar gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai zargin ta da kasa magance matsalolin tattalin arziki da kuma wahalhalun da miliyoyin 'yan Najeriya ke ciki.
A cewarsa, tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, ƙarfin sayen kayan masarufi yana raguwa, yayin da rashin aikin yi ke ƙara jefa iyalai cikin mawuyacin hali.
Hashim ya soki mulkin Tinubu
Hashim ya kuma yi zargin cewa masu mulki sun fi mayar da hankali kan yadda za su ci gaba da riƙe madafun iko maimakon warware matsalolin jama'a.
Ya ce haka kuma akwai wani yunƙuri na tsoma baki a cikin harkokin wasu jam'iyyun adawa domin raunana su kafin zaɓe mai zuwa.
Hashim ya bayyana rashin jin daɗinsa da wasu matakan da shugabannin jam'iyyarsa suka ɗauka dangane da burinsa na takarar shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa wannan mataki da suka dauka ya jawo tambayoyi kan gaskiya da kuma sahihancin tsarin da aka bi.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa shigarsa siyasa ba ta samo asali ne daga son zuciya ba, sai dai daga burin inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Ya nuna damuwa kan yadda iyaye da dama ke fama da wahala wajen biyan kuɗin makarantar 'ya'yansu, lamarin da ya sa wasu iyalai ke yin sadaukarwa mai raɗaɗi domin ci gaba da karatun yara.
Ana sa ran dake zaɓen Tinubu
A baya, mun wallafa cewa wata ƙungiyar wayar da kan matasa da ke da alaƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ta sanar da cewa ta koma APC.
A ranar Alhamis 4 ga watan Yuni, 2024, sanarwar ta ce tana goyon bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, tare da alƙawarin samar masa da ƙuri’u miliyan 10.
Ta bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da ita wanda kuma a nan fadi tsarinta na wayar da kan jama’a tare tabbatar da haɗuwarta da City Boy a ci gaba da shirin tunkarar 2027.
Asali: Legit.ng

