
Labaran duniya







Wata kotu a kasar Indonesia ta kama wata budurwa da laifin batanci ga annabi Isa a watan azumi. An daure ta a gidan yari kusan shekaru uku kan aikata laifin.

Amurka ta tallafa wa Najeriya da $763m a 2024, inda aka fi ba da muhimmanci ga kiwon lafiya, tsaro, tattalin arziƙi, ilimi da jin ƙai, kafin dakatar da USAID.

Wani jirgin kasa ya kusa yin ajalin wani dan kasar Peru yayin da ya kwanta a layin bayan ya kwankwadi barasa ya kwanta narci kansa na kan layin dogo.

Yawan makaman nukiliya a duniya ya karu yayin da ake fargabar barkewar Yaƙin Duniya na III. Tahoto ya bayyana yadda kasashe ke ƙara adadin makaman nukiliyarsu.

An kama wani matashi da laifin kashe mai kula da dandalin WhatsApp saboda ya cire shi a cikin dandalin ba tare da yi masa wani bayanin da ya gamsu ba.

Kasar Amurka ta yi Allah wadai da kisan da wasu 'yan bindiga suka yi wa Rabaran Sylvester Okechukwu kwana daya da sace shi. An kama faston ne a jihar Kaduna.

Sanata Peter Nwaebonyi mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a majalisar dattawa ya fito ya yi magana kan takaddamar Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio.

Yakin Ukreine da Rasha, zaman fargaba a Gabas ta Tsakiya da takun saka tsakanin Amurka da China ya kara jefa fargabar zuwan karshen duniya a 'yan kwanakin nan.

Gwamnatin Faransa ta jaddada aniyarta ta yaki da miyagun kwayoyi. Faransa za ta taimaka wa NDLEA wajen ba jami'anta horo da kwarewa a fannoni daban daban.
Labaran duniya
Samu kari