An Jibge Yan Sanda, Sojoji da Wasu Dakaru a Kewayen Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja

An Jibge Yan Sanda, Sojoji da Wasu Dakaru a Kewayen Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja

  • An kara tsaurara matakan tsaro a kusa da Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja gabanin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa
  • Fitaccen dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore na shirin jagorantar zanga-zangar neman ceto daliban da aka sace a Oyo da Borno
  • Hukumomin tsaro daban-daban sun jibge jami'ansu a wurare masu muhimmanci domin tabbatar da doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An tsaurara matakan tsaro a kewayen Fadar Shugaban Kasa da ke babban birnin tarayya Abuja yau Alhamis.

Hakan na zuwa ne yayin da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam, Omoyele Sowore, ke shirin jagorantar wata zanga-zanga domin neman a kubutar da daliban makarantu da aka sace a jihohin Oyo da Borno.

Aso Rock Villa.
Harabar fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa an jibge jami'an tsaro da dama wurare masu muhimmanci da ke kewaye da fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban APC, sun masa bidiyo yana neman agaji

Jami'an da aka gani suna siniti sun hada da na rundunar ‘yan sanda, sojoji, hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a

Zanga-zangar #OccupyAsoRock

An kara tsaron ne yayin da Sowore tare da magoya bayan jam’iyyar AAC da kungiyar Take It Back Movement ke shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar #OccupyAsoRock.

Ana sa ran zanga-zangar za ta tashi ne daga fin Eagle Square zuwa Fadar Shugaban Kasa domin jawo hankalin gwamnati kan halin da daliban da aka sace ke ciki.

Sowore ya bukaci gwamnati ta kara kaimi

Da yake magana gabanin zanga-zangar, Sowore ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara himma wajen tabbatar da ceto wadanda aka sace tare da daukar matakan magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.

Zanga-zangar ta biyo bayan rahotannin sace dalibai da malamai daga makarantu a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo da kuma wani harin sace dalibai a karamar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.

Daga cikin makarantun da abin ya shafa a Oyo akwai Community Grammar School, Baptist Nursery and Primary School da kuma L.A. Primary School da ke yankunan Esiele da Yawota.

Kara karanta wannan

An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027

Bayan faruwar lamarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga ta gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila zuwa yankunan da abin ya shafa.

Sowore.
Fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkin bil'adama, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Matakan da gwamnati ta dauka

Tawagar ta sanar da wasu matakai domin tabbatar da kubutar da wadanda aka sace da kuma kara tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana.

Daga cikin matakan akwai daukar masu gadin dazuka 1,000 aiki da kuma tura tawagar musamman domin gudanar da ayyukan ceto, kamar yadda Leadership ta kawo.

Ana sa ran wannan zanga-zanga za ta kara matsin lamba ga gwamnati wajen daukar karin matakai domin magance matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ke addabar makarantu da al'ummomi a Najeriya.

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro suka fatattaki masu zanga zangar neman a saki shugaban IPOB a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaron sun kama yan zanga-zagar ciki har da wani ɗan’uwan shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu da lauyansa.

Omoyele Sowore ya bayyana cewa ’yan sanda sun kuma kama wasu mutane marasa laifi da ke wajen yayin da suke tarwatsa masuNzanga-zangar da ke neman a saki Kanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262