Kungiyar Yan Ta'adda Ta Kafa Hujja da Kalaman Sheikh Jingir kan Zaben Musulmi da Musulmi

Kungiyar Yan Ta'adda Ta Kafa Hujja da Kalaman Sheikh Jingir kan Zaben Musulmi da Musulmi

  • IPOB ta ce kalaman da ake dangantawa da Sheikh Sani Yahaya Jingir sun sake farfado da damuwar Nnamdi Kanu kan ‘yancin addini a Najeriya
  • Kungiyar 'yan ta'addan ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta fayyace matsayinta kan daidaiton ‘yancin Musulmi, Kirista da masu wasu addinai daban-daban
  • Yan ta'addan IPOB sun kuma sake kalubalantar ci gaba da tsare Nnamdi Kanu, inda ta bayyana cewa batun ya shafi bin doka, adalci da ‘yancin dan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu – Kungiyar 'yan ta'addan IPOB ta ce kalaman da aka danganta ga Sheikh Sani Yahaya Jingir kan matsayin addini a Najeriya sun tabbatar da wasu daga cikin gargadin da jagoranta, Mazi Nnamdi Kanu.

Kungiyar ta bayyana cewa dama Nnamdi Kanu wanda a yanzu haka aka garkame kan laiffukan ta'addanci, ya dade yana magana kan ‘yancin addini da daidaito tsakanin ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun

IPOB ta dura a kan Jingir
Jagoran JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Jaridar vanguard ta kawo laabarin cewa kakakinta, Emma Powerful, ya fitar ranar Talata, 11 ga watan Agusta, 2026 kungiyar ta ce ana zargin an bayyana Najeriya a matsayin kasar Musulmi, tare da kiran Kiristoci da kafirai.

IPOB ta fusata kan kalaman Jingir

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa IPOB ta ce kalaman sun haifar da damuwa game da alkawarin kundin tsarin mulkin kasar na tabbatar da daidaiton ‘yancin addini.

Yan ta'addan IPOB sun ce bai kamata a dauki irin wadannan kalamai a matsayin magana kawai ba, inda aka bayyana cewa tsarin Najeriya ya tanadi ‘yancin kowane dan kasa ba tare da la’akari da addininsa ba.

Kungiyar ta ce kalaman sun sake ba da muhimmanci ga abin da ta bayyana a matsayin gargadin da Kanu ya dade yana yi kan yiwuwar sauya yanayin siyasa da addini na Najeriya.

Bukatar yan ta'addan IPOB ga gwamnati

IPOB ta ce lokacin musanta wadannan damuwa ya wuce, tare da bukatar Gwamnatin Tarayya ta bayyana matsayinta kan daidaiton addinai da kuma matsayin Najeriya a matsayin kasa mai bin kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

An tsare tsohon jami'in DSS a gidan kaso kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci

IPOB na neman a tuhumi kalaman Jingir
Wasu daga cikin yan ta'addan IPOB dauki da tutocinsu Hoto: IPOB
Source: Twitter

Haka kuma, kungiyar ta sake sukar gurfanar da Kanu da ci gaba da tsare shi, tana mai cewa lamarin ya haifar da tambayoyi kan bin ka’idojin shari’a da kuma bin doka.

IPOB ta yi nuni da hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 13 ga Oktoba, 2022, wanda ta ce ya bayar da umarnin sakin Kanu, tare da tambayar yadda wasu matakai na shari’a suka kai ga ci gaba da tsare shi da kuma hukuncin da aka yanke masa daga baya.

Fasto ya caccaki kalaman Jingir

A baya, mun samu labarin cewa Primate Elijah Ayodele ya soki gwamnatin tarayya kan zargin yin shiru game da kalaman da ake dangantawa da Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Primate Ayodele ya ce ya kamata a kama Sheikh Jingir saboda kalaman da ya yi, yana gargadin cewa hakan na iya barazana ga zaman lafiya a fadin kasar da ake ganin tana muzgunawa Kiristoci.

Shugaban cocin ya bukaci gwamnatin Tinubu ta gargadi shugabannin addini kan kalaman da ka iya haddasa rikicin addini wanda yana daya daga cikin abubuwan da ke jawo matsala a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng