Gwamna Makinde Ya Samu Tikitin Takara, Zai Gwabza da Atiku da Tinubu a Zaben 2027

Gwamna Makinde Ya Samu Tikitin Takara, Zai Gwabza da Atiku da Tinubu a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM a babban zaɓen 2027
  • Shugaban APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ya miƙa masa takardar shaidar cin zaɓe da tutar jam’iyya a wani taro da ya gudana yau Asabar
  • Dantalle ya ce nasarar Gwamna Makinde ta nuna fara wani sabon yunƙuri na sake gina Najeriya da haɗin kan masu neman sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM domin fafatawa a babban zaɓen shekarar 2027.

Makinde ya samu tikiti ne bayan kammala tsarin zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar ta gudanar, inda daga bisani aka miƙa masa takardar shaidar nasara tare da tutar APM.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya girma, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde yana magana a taron hadaka da jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

An miƙa wa Seyi Makinde takardar nasara

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an gudanar da taron bayyana ɗan takarar ne a dakin taro na Emeritus Professor Theophilus Ogunlesi Hall da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shugaban APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ne ya miƙa wa Makinde takardar shaidar cin zaɓe da kuma tutar jam’iyyar a gaban wakilai daga jihohi daban-daban na ƙasar nan.

Kafin ya miƙa tutar, Dantalle ya gayyaci shugabannin jam’iyyar APM na jihohi 36 tare da neman amincewarsu kan bai wa Makinde tikitin shugaban ƙasa.

Wakilan sun nuna amincewa da ƙarfi ta hanyar kuri’ar murya, lamarin da ya tabbatar da goyon bayan da Gwamna Makinde yake samu a cikin jam’iyyar.

Yusuf Dantalle ya yaba wa Makinde

Da yake jawabi, Dantalle ya bayyana cewa an zaɓi Makinde ne saboda tarihin ayyukansa da kuma yadda ya jagoranci jihar Oyo cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Kara karanta wannan

Peter Obi ko Kwankwaso: NDC ta shirya tsaida 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2027

Ya ce gwamnan ya nuna ƙwarewa, jajircewa da kuma himma wajen inganta rayuwar al’umma, abin da ya sa jam’iyyar APM ta ga ya dace ya jagoranci tafiyar neman shugabancin ƙasa.

A cewarsa, fitowar Makinde a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa alama ce ta fara wani sabon salo na siyasa da ya kira “Reset Nigerian Movement”, wato yunƙurin sake farfaɗo da Najeriya.

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a taron hadakarsu da jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Sabuwar haɗaka domin canza Najeriya

Dantalle ya kuma bayyana cewa takarar Makinde na wakiltar wata sabuwar haɗaka tsakanin wasu ƙungiyoyin siyasa da masu ruwa da tsaki da ke son ganin an samu sabuwar alkibla a tafiyar Najeriya.

Ya ce dubban ‘yan Najeriya na neman shugabanci mai adalci, haɗin kai da ci gaba, kuma suna ganin Makinde na da damar bayar da irin wannan shugabanci,cewar rahoton Leadership.

Za a fafata da hadimin Atiku a 2027

A wani labarin, kun ji cewa tsohon hadimin Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugabanNkasa na jam'iyyar ADP a babban zaben 2027 da ke tafe.

An tabbatar da nasarar Ambasada Aliyu Bin Abbas ne a safiyar Asabar yayin babban taron jam'iyyar na ƙasa da aka gudanar a birnin Abuja.

Aliyu Bin Abbas ya taɓa zama hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar , wanda shi ma yanzu yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262