Atiku Abubakar Ya Bayyana Tsawon Lokacin Da Zasu Kwashe Suna Zanga-Zanga
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zasu kwashe suna zanga-zangar da suke yi
- Jam'iyyar PDP dai ta fara gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda jam'iyyar APC ta samu nasara
- Atiku Abubakar ya kuma tabbatar da cewa duk da zanga-zangar da suke yi, za kuma su je kotu domin neman haƙƙin su
Abuja- Dan takarar kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a ranar Litinin ya bayyana cewa jam'iyyar zata cigaba da zanga-zangar da take yi kullum har na tsawon lokaci.
Atiku, wanda yayi magana lokacin da ya jagoranci zanga-zangar da jam'iyyar take yi zuwa hedikwatar hukumar INEC, yace zanga-zangar ba zata hana su zuwa kotu ba domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar. Rahoton The Nation

Source: UGC
Jam'iyyar ta kuma miƙa takardar koke ga hukumar zaɓen mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Barr. Festus Okoye, kwamishin labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a na ƙasa na hukumar shine ya amshi takardar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku ya jagoranci sauran shugabannin jam'iyyar domin nuna adawar su kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta lashe.
“Muna yin zanga-zanga sannan muna da dukkanin ƴancin yin zanga-zanga. Duk da cewa muna zanga-zanga hakan ba zai dakatar da mu daga zuwa kotu ba. Zamu yi zanga-zanga mai tsawo. Ko kullum ko duk bayan kwana ɗaya.
Sauran waɗanda suke a cikin masu zanga-zangar akwai shugaban jam'iyyr na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu, tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Prince Uche Secondus; gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal. Rahoton Daily Post
Sauran sun haɗa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; Kola Ologbondiyan, Daniel Bwacha, sanata Dino Melaye da sauran su.

Kara karanta wannan
Goyon Bayan Tinubu: Ɗan Takarar Gwamnan Labour Party Na Ruwa, Jam'iyyar Na Shirin Juya Masa Baya
Dan Shekara 27 Daga Arewa Ya Ajiye Tarihin Zama ‘Dan Autan ‘Yan Majalisar Tarayya
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ɗan Arewacin Najeriya, ya kafa sabon tarihi a majalisar wakilai ta Najeriya.
Matashin wanda ya fito daga jihar Ƙebbi ya kafa wannan tarihin ne a.zaɓen da ya gabata.
Asali: Legit.ng
