Jerin Matan Arewa 4 da Jam'iyyar APC Ta Tsaida Takarar Majalisar Wakilai a Zaben 2027
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kammala zabukan fitar da gwani da 'yan takararta a dukkan matakai yayin da zaben 2027 ke kara kusantowa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A kokarinta na jawo mata a harkokin gudanar da mulkin Najeriya, jam'iyyar APC ta bai wa mata tikitin takarar Majalisar tarayya a mazabu daban-daban a Najeriya.

Source: Twitter
'Daya daga cikin matan da aka tsaida takara da suka ja hankali ita ce Hajiya Jamila Abdu Mani daga jihar Katsina, kamar yadda tashar Channels tv ta rahoto.
Hajiya Jamila ta samu tikitin neman kujerar 'dan Majalisar wakilai na mazabar Mani da Bindawa a zaben 2027.
Mata na fuskantar kalubale a Arewa
Sai dai duk da fafutukar da mata ke yi na ganin an ware masu 35% na kujeru a Majalisar tarayya, har yanzu ba su samun damarmakin tsayawa takara yadda suke so.
A Arewacin Najeriya, mata na fuskantar kalubale da ya danganci addini, inda malamai ke ba da fatawowi mabanbanta kan halastcin bai wa mace shugabanci a addinin musulunci.
Wasu malaman na ganin za a iya ba mace damar zama yar Majalisar, kwamishina ko wani mukami a gwamnati, amma ba za a bari ta zama shugaban kasa ko gwamna ba.
Matan Arewa 4 da suka samu tikitin APC
Legit Hausa ta tattaro muku matan da APC ta tsaida takarar kujerar Majalisar wakilai a Arewacin Najeriya gabanin babban zaben 2027. Ga su kamar haka:
1. Hajiya Jamila Abdu Mani
Mace daya tilo da ta fito neman takara a jihar Katsina, Hajiya Jamila Abdu Mani ta samu nasarar zama yar takarar Majalisar wakilai a inuwar APC.
Hajiya Jamila, tsohuwar Mai ba gwamnan Katsina shawara kan ilimin 'ya'ya mata, ta lashe tikitin jam’iyyar APC na mazabar Bindawa/Mani ta tarayya a zaben shekara mai zuwa.

Source: Facebook
Ta samu wannan nasara ne a zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar 16 ga watan Mayu, 2026, inda ta kayar da dan Majalisa mai ci, Hon. Ahmed Saleh, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan
An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027
2. Hajiya Fati Kakenna
Premium Times ta ruwaito cewa Hajiya Fati Kakenna Monguno ta samu tikitin APC na takarar Majalisar wakilai a mazabar Abadam, Kukawa, Guzamala da Mobbar ta jihar Borno a zaben 2027.
An tabbatar da ita ne a wani taron sulhu na masu ruwa da tsaki da ya samu halartar dattawan jam’iyya, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin APC, da kuma shugabannin mata da matasa daga Arewacin Borno.

Source: Facebook
A jawabin karbar takarar, Fati Kakenna ta gode wa Gwamna Zulum da shugabannin Arewacin Borno bisa amince da ita.
Ta yi alkawarin samar da ingantaccen wakilci, karfafa hadin kai da kuma kare muradun al’ummar mazabarta idan ta samu nasara a zaben 2027.
3. Regina Akume
Hon. Regina Akume, matar Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ta samu tikitin APC domin sake neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka a Jihar Benue.
Regina Akume ta samu nasarar ne a zaben fitar da gwani na majalisar tarayya da APC ta gudanar a fadin jihar gabanin babban zabe mai zuwa, kamar yadda The Cable ta kawo.

Source: Facebook
Duk da nasarar da Regina Akume ta samu, rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan siyasa da ake ganin suna da alaka da Sanata George Akume sun kasa samun tikitin jam’iyyar APC a zabukan fitar da gwani.
4. Hon. Blessing Onuh
Blessing Onuh, ‘diyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban jam’iyyar ADC na kasa, David Mark, na cikin matan da suka samu tikitin takarar APC a Arewacin Najeriya.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Blessing Onuh ta samu tikitin jam’iyyar APC domin sake neman kujerar Majalisar wakilai a babban zaben 2027.
Sakamakon lashe zaben fitar da gwani na APC, 'yan Majalisar za ta nemi tazarce a mazabar Otukpo/Ohimini ta Jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya.

Source: Facebook
Gwamnoni 7 da suka samu tikitin sanata a APC
A wani labarin, kun ji cewa akalla gwamnoni bakwai da wa'adinsu zai kare a 2027 sun samu tikitin takara a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Gwamnonin sun samu tikitin takara ne bayan lashe zabukan fitar da gwani a mazabunsu yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.
Daga cikin wadannan gwamnoni akwai Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da takwaransa na jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


