Duka Bayanan da Suka Fito daga Juyin Mulkin da Aka Yi Yunkurin yi wa Tinubu
- Sojoji da fararen hula sun kulla juyin mulki sakamakon matsin rayuwa da rashin inganta jin dadin jami’an kasar
- An fahimci wanda ya jagoranci shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu ya fusata ne bayan an ki kara masa girma
- Binciken takardu ya nuna an kashe miliyoyin nairori ga sojoji, 'yan kasuwa, da malamai kafin a dakile shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - ‘Yan Najeriya da dama sun dauka labarin kanzon kurege ne a lokacin da suka ji cewa an yi kokarin shirya juyin mulki a 2025.
Bayan shekara da shekaru rabon da a ji sojoji a kan mulki, an samu wasu jami’an da suka yi damarar su kifar da gwamnatin farar hula.

Source: Getty Images
Wasu rahotanni da aka shafe kusan makonni uku ana fitar wa a jaridar Premium Times sun fitar da bayanin yunkurin juyin mulkin.

Kara karanta wannan
Da gaske ne: Trump ya tabbatar da fargabar harin Iran, ya yi basaja a cikin jirgi
Wane ne wanda ya shirya juyin mulkin?
Bincike ya nuna cewa Mohammed Ma’aji wanda Kanal ne a gidan sojan kasa, shi ne ya kitsa yadda za a kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Bayanan da ya yi da kan shi sun nuna yadda ya dauki wannan aniya da ya fadi jarrabawar zama Birgediya Janar sau biyu a 2023 da 2024.
Kanal Ma’aji ya fake da matsalar tsaro, rashin gaskiya da sauran matsaloli wajen ganin an hambarar da gwamnati, sai shi ya dare kan mulki.
Shirye-shiryen kifar da gwamnatin Bola Tinubu
Wadanda suka yi wannan shiri sun saye motoci na musamman kuma sun raba aiki tun daga barikin sojoji, filin jirgin sama zuwa fadar Aso Rock.
Akwai wadanda aka ba alhakin shiga gidan rediyo da an yi nasarar kifar da gwamnati. Sun rika amfani da wani yare ne wajen shirye-shiryen nasu.
Ba a tsaida lokaci na karshe ba amma an yi tunanin ranakun 27 ga Satumba da 1 da kuma 4 ga watan Oktoban 2025 wajen yin aika-aikar.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa
Idan da sun yi nasara, za su karbe mulki ne tsakanin 1:00 zuwa karfe 2:00 na tsakar dare.
Ana tunanin wannan ya sa Bola Tinubu ya yi watsi da jawabin da Shugaban kasa ya saba gabatarwa a 1 ga Oktoba domin murnar samun yanci.
Kayan aikin da aka tanada a juyin mulki
Sojojin sun shirya tanadan makamai da motoci daga barikin sojoji. A shirin har da amfani da tubabbun ‘yan Boko Haram da ‘yan sa-kai.
An gano yadda Jami’an sojoji irinsu Laftanan Kanal Shamsudeen Bappah suka yi wa Ma’aji alkawarin samar masa da dakaru da kayan aiki.
Ta ina aka samu kudin juyin mulkin?
Wajen harkar kudi kuwa, an ji rawar da Timipre Sylva ya taka. An yi lissafin cewa za a bukaci N5bn kafin a iya ganin bayan gwamnatin.
An tura makudan miliyoyi ta hannun kamfanin Purple Waves Limited da wani ‘dan canji. A Satumban 2025 aka rika raba wadannan kudi.
Rawar da malamai da 'yan wasa za su taka
Domin a yi nasara, malaman addini irinsu Goni Bukar sun taimaka da addu’a kuma an biya shi kudi N50m kamar yadda bincike suka nuna.

Kara karanta wannan
Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Yanzu haka akwai malamai irinsu Sheikh Khalifa Zariya wadanda suke a daure saboda zargin.

Source: Getty Images
Baya ga addu’o’i da malamai za su yi, an nemi gudumuwar tsohon ‘dan wasan kwaikwayo, Stanley Amandi ya yada furofaganda.
Abin da aka nufa shi ne a yi kokarin cusa wa mutane a ran su cewa ya kamata jama’an Najeriya su yi maraba da dawowar sojoji a mulki.
An bukaci Amadi ya shirya bukukuwan murna, ya tattaro masu fada-a ji a kafafan sada zumunta kuma ya yada sakonnin maraba da juyin.
Rabon mukamai idan an yi juyin mulki
Rahoton ya ce da an kai ga yin nasara, da Ma’aji zai zama shugaban kasa kuma akwai yiwuwar Manjo Ilyasu Jamilu ya zama babban dogaran sa.
Akwai Felix wanda aka yi alkawarin minista, shi kuma S. Bappah ya nemi ya shugabanci EFCC.
Amma a Satumban 2025 aka kama shi da yaudarar zai gana da hafsun sojojin kasa, Janar Olufemi Oluyede a game da lamarin karin girman shi.
Tun daga lokacin ba a kara jin labarin Kanal Ma’aji da yunkurinsu na kifar da gwamnati ba.
Zargin juyin mulki ya ci malamin Musulunci
An gurfanar da wani malamin Musulunci, Sheikh Bukar Kashim Goni, a kotu bisa zargin kasancewarsa da hannu a shirin kifar da gwamnati.
Malamin ya tabbatar da cewa ya karɓi fiye da Naira miliyan 10 daga hannun babban wanda ake zargi, Kanal Mohammed Ma’aji ya yi addu’a.
Masu bincike sun ƙalubalanci bayaninsa da shaidun banki da ke nuna an fara tura masa kuɗin tun watanni bayan hawan Bola Ahmad Tinubu.
Asali: Legit.ng
