Lokuta 6 da Atiku Ya Nemi Samun Kujerar Shugaban Kasa da Yadda Takarar Ta Kasance
QFCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ba bakon suna ba ne wajen neman shugabancin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Atiku Abubakar ya sha gwada sa'arsa wajen neman kujerar shugaban kasa ta Najeriya tun daga shekarar 1993.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta rahoto cewa Atiku zai yi takarar shugaban kasa a zaben 2027, bayan ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC.
Ana ta damawa da Atiku Abubakar a siyasa
Atiku Abubakar ya kasance dumu-dumu cikin harkokin siyasar Najeriya a tsawon shekaru 30 da suka gabata.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya dade yana fafutukar siyasa tare da yunkurin neman shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyu daban-daban.
Lokutan da Atiku ya nemi shugabancin Najeriya
Atiku Abubakar ya fara neman takara a jam'iyyar SDP a 1993, inda daga baya ya yi takara a jam'iyyun AC, APC da PDP.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta tsorata, ta ce Peter Obi zai iya ba Atiku mamaki a zaben 2027
Ga jerin lokutan da Atiku ya yi takara a kasa:
1. Zaben fitar da gwani da su Abiola
Atiku ya fara gwada sa'arsa ta takarar shugaban kasa a lokacin da aka yi yunkurin mayar da Najeriya karkashin mulkin dimokuradiyya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Ya nemi tikitin yin takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP, inda ya kece raini a zaben fitar da gwani da Moshood Abiola da Ambasada Babagana Kingibe, tashar BBC Hausa ta taba kawo rahoton.
Moshood Abiola ne ya yi nasara da kuri'a 3,617 a zaben fitar da gwanin yayin da Atiku ya samu kuri'a 2,066.
Sai dai, rahotanni sun nuna cewa daga baya Atiku ya hakura, tare da bukatar magoya bayansa su goyi bayan Moshood Abiola duk Abiola ya zabi Kingibe a maimakon shi.
2. Fafatawa da Umaru Musa Yar'adua
Bayan yin mataimakin shugaban kasa na shekara takwas, Atiku Abubakar, ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Atiku ya yi yunkurin maye gurbin Shugaba Olusegun Obasanjo, a karkashin inuwar PDP amma sai lamarin ya ci tura.

Kara karanta wannan
Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"
Daga baya sai ya yi tsalle ya koma jam'iyyar AC inda ya yi hada kai da Bola Tinubu, wanda hakan ya sanya fafata da Umaru Musa Yar'Adua na jam'iyyar PDP.
Jaridar The Punch ta ce a sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar, Yar'Adua ya samu nasara inda ya samu kuri'a 24,638,063.
Hakazalika, tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari wanda ya yi takara a inuwar jam'iyyar ANPP a wancan lokacin ya zo na biyu da kuri'a 6,605,299, yayin da Atiku ya zo na uku da kuri'a 2,637,848.
3. Fafatawa da Jonathan wajen neman tikitin PDP
Atiku ya yi kokarin samun tikitin jam'iyyar PDP a zaben 2011, inda ya fafata da Shugaba Goodluck Jonathan wanda ke kan kujerar a wancan lokacin a zaben fitar da gwani.
A zaben fitar da gwanin, Goodluck Jonathan ya lallasa Atiku inda ya samu kuri'a 2,736, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ya samu kuri'a 805, The Guardian ta kawo labarin a lokacin.
Dattawan Arewa sun zabi Wazirin Adamawa ya kara da shugaban kasa mai-ci wajen neman tikitin PDP lokacin.
4. Takara da Buhari a zaben fitar da gwanin APC
Atiku ya sake gwada sa'arsa ta neman shugaban kasa inda ya fice daga PDP zuwa sabuwar jam'iyyar hadaka ta APC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fafata da manyan masu neman kujerar irinsu Muhammadu Buhari, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaben fitar da gwani na APC.
Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwanin da kuri'a 3,430, Rabiu Musa Kwankwaso ya zo na biyu da kuri'a 974, yayin da Atiku ya zo na uku da kuri'a 954, a lokacin rahoton ya zo a jaridar Vanguard.
5. Atiku ya yi takara da Buhari a zaben 2019
Atiku Abubakar ya bar APC zuwa jam'iyyar PDP inda ya samu tikirin fafatawa da Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Jaridar Premium Times ta ce a sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar, Muhammadu Buhari ne ya samu nasara da kuri'a 15,191,847, inda ya lallasa Atiku wanda ya samu kuri'a 11,262,978.
A zaben ne 'dan siyasar ya dauko Peter Obi domin ya zama abokin gaminsa, kuma ya samu makudan kuri'un da bai taba samu ba a lokacin.

Kara karanta wannan
2027: NDC ta jawo tsohon shugaban matasan APC, ta tsaida shi takarar gwamna a Gombe

Source: Twitter
6. Tinubu ya kayar da Atiku a 2023
Tsohon mataimakin shugaban kasar bai gaji ba, domin ya sake gwada sa'arsa a zaben 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
A wancan lokacin Atiku ya fafata da dan takarar APC, Bola Tinubu, Peter Obi na LP da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP.
Shugaba Tinubu ne ya yi nasara da kuri'a 8,794,726, yayin da Atiku ya zo na biyu da 6,984,520 kamar yadda hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben, tashar BBC ya nuna hakan.
Atiku ya tattauna da Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Atiku ya bayyana cewa tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki musamman matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.
'Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC a zaben 2027, ya ce shi da Amaechi sun yi doguwar tattaunawa kan yadda Najeriya ke fuskantar kalubale masu yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
