'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban APC, Sun Masa Bidiyo Yana Neman Agaji

'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban APC, Sun Masa Bidiyo Yana Neman Agaji

  • Al'umma na cigaba da nuna bacin rai kan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sadarwa, inda 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu dattawa
  • Wani rahoto ya nuna cewa daya daga cikin mutanen biyu da aka kama tsohon shugaban jam'iyyar APC ne a karamar hukumar Koko/Besse
  • Mutane biyun sun yi magana suna rokon da kubutar da su daga hannun masu garkuwan da suka sace su ta hanyar biyar kudin fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Ana cigaba da muhawara kan kama wasu dattawa biyu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka yi a jihar Kebbi.

Bidiyon ya bayyana ne a daidai lokacin da ake korafi kan sace dalibai a jihohin Oyo, Borno, Zamfara da sauransu, lamarin da ya kai ga zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Da gaske 'yan bindiga sun sako dalibai da malamai da suka sace a Oyo? Bayanai sun fito

Wadanda aka sace a Kebbi
Tsohon shugaban APC a Kebbi da abokin shi da aka sace. Hoto: Dan Katsina
Source: Facebook

An kama tsohon shugaban APC

'Dan Katsina da ke sharhi kan lamuran tsaro ya wallafa biyon mutane suna kira ga wasu jama'a su ceto su a sokon da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya ce:

"Wannan bidiyon na nuna tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi tare da wani abokinsa yayin da ’yan bindiga ke wulaƙanta su a dajin Birnin Gwari."
"Baya ga irin mummunar mu’amalar da aka yi wa waɗannan mutanen, bidiyon ya sake tayar da hankali kan yadda ƙungiyoyin ’yan bindiga ke ci gaba da gudanar da ayyukansu a sassan Arewacin Najeriya.
"Me ke ba wa waɗannan masu aikata laifuka ƙarfin gwiwar ba kawai yin irin waɗannan abubuwa ba, har ma su ɗauki bidiyon waɗanda suka kama sannan su sake shi ba tare da wata alamar tsoron hukumomin tsaro za su gano su ba?"

Kiran da mutanen suke yi daga jeji

Kara karanta wannan

Buratai ya yi tone tone kan 'yan siyasa game da rashin tsaron Najeriya

Mutanen da aka kama, daya daga cikinsu ya ce shi tsohon shugaban APC ne, dayan kuma ya bayyana cewa shi malamin makaranta ne.

Sun yi kira da a taimaka musu suna cewa ba su da lafiya:

"Idan so kuke mu mutu, sai ku fada mana mu yi sallama da ku mu mutu. Yanzu ga Yahaya nan ba shi dalafiya. Ni ma ka san ba ni da lafiya, kullum sai na sha magani."
'Kwanan mu nawa muna tafiya a kasa, duk mun wahala.
"Don Allah ku tashi tsaye, a taimaka."

Ga bidiyon korafin da suka yi da Babangida ya wallafa a X:

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ra’ayoyin jama’a kan lamarin

Jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyi game da biyon mutanen, inda wasu ke cewa hakan ya nuna yadda rashin tsaro ya yi kamari.

A Sadiq ya ce:

“Abin takaici ne ganin yadda wannan wahala ta daɗe tana ci gaba."

Menelik II ya ce:

“Shin kyawawan manufofin APC sun shafi tsohon shugaban jam’iyyar a ƙaramar hukumar Koko/Besse ta jihar Kebbi?”

Makamai sun zo Najeriya daga Libya

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Cutar kwalara ta kama mutane sama da 4,000 a Borno, an rasa rayuka

A wani labarin, kun ji cewa majalisar dinkin duniya ta yi zama na musamman game da yaduwar makamai a fadin duniya.

Wata jami'ar majalisar ta bayyana cewa makamai da dama sun bazu daga Libya zuwa Najeriya da wasu yankunan Afrika.

Ta bayyana cewa shekaru bayan yakin Muammar Gaddafi, makaman na cigaba da haifar da rashin tsaro a yankunan duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng