Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa
- Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tuna da tsohon Shugaba Umaru Yar'adua a yayin da yake cika shekaru 11 da rasuwa
- Jonathan ya bayyana Yar'Adua a matsayin shugaban mai hangen nesa, son zaman lafiya da haɗin kai
- Goodluck Jonathan ya ce duk da rasuwar tsohon mai gidansa shekaru 11 da suka wuce, har yanzu ba a manta da ayyukan alheri da ya yi ba
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, a ranar Laraba, ya bayyana marigayi Shugaba Umaru Yar'adua a matsayin mutum mai hangen nesa.
Ya ce fatan Yar'adua shine samar da zaman lafiya da haɗa kan ƴan Nigeria.
DUBA WANNAN: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama
Marigayi Ƴar'Adua ya rasu shekaru 11 da suka gabata a lokacin yana kan mulki.
Jonathan, a shafinsa na sada zumunta ya ce, "A yau, ina jinjina ga mai gida na, abokina, abokin aiki kuma ɗan uwa, Shugaba Umaru Musa Yar'adua wanda ya bar wannan duniyar shekaru 11 da suka gabata.
"A matsayin mu na ƴan siyasa, munyi tarayya a ƙoƙarin mu na gina ƙasa inda akwai zaman lafiya da haɗin kai. Ƴar'Adua ya mutu yana ƙoƙarin cimma wannan manufar ta haɗa kan ƴan Nigeria.
"Duk da cewa baya tare da mu, ba za mu taɓa mantawa da ayyukan da ya yi ba.
KU KARANTA: Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago
"Za mu cigaba da tunawa da shi a matsayin mutum mai son zaman lafiya, mai ƙoƙarin gina ƙasa kuma wanda ya siffantu da ginshikin demokradiyya na yi wa mutane hidima, zaman lafiya, gaskiya da ƙauna."
A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.
Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.
Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.
Asali: Legit.ng