Siyasa
Dan takarae gwamnan jihar Bayelsa na jam'iyyar LP, Udengs Eradiri da mataimakinsa sun sanar da ficewa daga jam'iyyar. Ya fadi inda zai koma nan gaba.
Shugabannin NNPP na jihohin Kudu maso Kudu sun musanta raɗe-raɗin da ake cewa rigima ta raba jam'iyyar gida biyu, sun ce Kwankwaso ne jagoran jam'iyya na ƙasa.
Kungiyar kabilar Igbo (Ohanaeze Ndigbo) ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan kalamansa game da zaben 2027 da ake tunkara.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa a yanzu ya yarda cewa ɗansa ya cancanci riƙe mukamin gwamnati saboda ya girma .
Hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu na musamman, Daniel Bwala ya koka kan yadda wasu ke kwatanta Najeriya da kasar Ghana inda ya ce kasashe ba daya ba ne.
Gwamnatin jihar Benue ga ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa tana nuna wariya ga wasu yan Majalisar dokoki masu goyon bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Yayin da ake cigaba da rigima kan sarauta a Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nuna takaici kan yadda ake kwatanta jihar tana dauke da sarki biyu da kuma gwamna biyu.
Bayan gwamna ya rikice yayin gabatar da kasafin kudi a gaban Majalisa, shugaban APC a Edo, Jarrett Tenebe ya kare Gwamna Monday Okpebholo na jihar.
Masanin siyasa, Farfesa Adele Jinadu ya zargi 'yan siyasa da fara shirin murde zaben 2027. Ya ce fara nada 'yan siyasa a INEC alama ce ta cewa za a yi magudi.
Siyasa
Samu kari