PDP Ta Motsa a Kano, Ta Ɗauki Matsaya game da Takarar Jonathan a 2027

PDP Ta Motsa a Kano, Ta Ɗauki Matsaya game da Takarar Jonathan a 2027

  • PDP reshen jihar Kano ta cimma matsayarta a kan mara wa dan takarar shugaban kasa da tsagin Tanimu Turaki ya fitar yayin da rikici ya dabaibaye jam'iyyar
  • Shugaban PDP na Kano, Yusuf Ado Kibiya, ya ce jam'iyyar ta amince da matakin da shugabancin ƙasa ya ɗauka bisa tanadin kundin tsarin mulki
  • Jam'iyyar PDP na da 'yan takarar shugaban kasa guda biyu - tsohon shugaba Goodluck Jonathan na tsagin Turaki da Sandy Onor na tsagin Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ta sake tabbatar da goyon bayanta ga takarar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

Ta ce wannan matakin da ta dauka shi ne ke tabbatar da cewa tana mutunta hukuncin da shugabancin jam'iyyar na ƙasa ya yanke kan batun.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala Muhammad ya yi bayani game da hada takara da Jonathan a PDP

PDP a Kano ta mara wa Jonathan baya
Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan a yayin wani taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Shugaban PDP na Kano, Yusuf Ado Kibiya, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin 1 ga watan Yuni, 2026 yayin taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam'iyyar da ke Kano.

Kano: PDP ta goyi bayan Jonathan

The Guardian ta ruwaito cewa Yusuf Ado Kibiya ya ce reshen Kano ya yi nazari kan matakin da kwamitin zartarwa na ƙasa na jam'iyyar ya ɗauka dangane da takarar Jonathan, kuma ya tabbatar da cewa suna ci gaba da bin tsarin doka da ƙa'idojin jam'iyyar.

Ya ce:

"PDP ta Kano ta yi nazari kan matakin da shugabancin jam'iyyar na ƙasa ya ɗauka game da takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan."
PDP ta nemi hadin kan yayanta a Kano
Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban Najeriya Hoto; Goodluck Jonathan
Source: Facebook

A cewarsa, reshen Kano ya amince da dukkannin matakan da suka kai ga wannan matsaya, yana mai jaddada cewa dole ne a mutunta hanyoyin da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada a kowane mataki.

Kara karanta wannan

Martanin Kwankwaso bayan samu tikitin takarar mataimakin Peter Obi a NDC

Yusuf Ado Kibiya ya ƙara da cewa:

"Mun amince kuma muna mutunta tsarin da ya kai ga wannan hukunci, sannan muna goyon bayan haƙƙin shugabancin ƙasa na tsara alkiblar jam'iyyar bisa kundin tsarin mulki da dokokin da ke jagorantar ta."

PDP ta nemi hadin kan 'ya'yanta

Yusuf Ado Kibiya ya kuma yi kira ga dukkannin 'ya'yan jam'iyyar su zama masu haɗin kai, biyayya da kuma sadaukar da kai wajen cimma muradun PDP.

Ya tabbatar wa magoya bayan jam'iyyar cewa duk da sauye-sauyen siyasa da kuma sauya sheƙar wasu 'yan siyasa zuwa wasu jam'iyyu, PDP a Kano na nan daram da karfinta.

Har ila yau, shugaban ya sake jaddada aniyar PDP na ci gaba da kare ƙimar dimokuraɗiyya, riƙon amana da hidimar jama'a.

Tsagin PDP ya ba Jonathan tuta

A baya, mun kawo labarin cewa duk da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, an ayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa na zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan ya fice daga APC, Omo Agege ya samu takara a jam'iyyar NDC

Jam'iyyar ta tabbatar da takarar Jonathan ne a taron musamman da aka gudanar a Abuja, inda Fred Agbedi ya karbi takardar shaidar nasara a madadinsa domin Jonathan bai samu damar halartar taron ba.

Bayan jami’an tsaro sun hana shiga wurin taro na farko, shugabannin bangaren PDP sun sauya wuri tare da alkawarin sanar da ranar mika tuta tare da sukar Nyesom Wike da zargin hana ruwa gudu a tsagin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng