'Dan Gwagwarmaya Sowore Ya Fito Takarar Shugaban Kasa, Zai Kara da Tinubu a 2027

'Dan Gwagwarmaya Sowore Ya Fito Takarar Shugaban Kasa, Zai Kara da Tinubu a 2027

  • Omoyele Sowore ya bayyana cewa zai sake neman kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2027 karkashin jam’iyyar AAC
  • 'Dan gwagwarmayar ya ce Najeriya na cikin mawuyacin hali, yana mai cewa tsofaffin ‘yan siyasa ne suka jefa kasar cikin talauci da rashin tsaro
  • Sowore ya ce yana da manufofi da dabarun da za su ceto Najeriya daga halin da take ciki fiye da na Shugaba Bola Tinubu da sauran ‘yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A yayin da ake tunkarar zabukan 2027, an sake samun 'dan takarar da zai kara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a neman kujerar shugaban kasar Najeriya.

'Dan gwagwarmaya mai kare hakkin bil’adama kuma mamallakin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben.

Kara karanta wannan

ADC ta fitar da sanarwa, Atiku na shirin fafatawa da masu neman takarar 2027

Omoyele Sowore ya bayyana kudurinsa na neman takarar shugaban kasar Najeriya.
Omoyele Sowore, dan gwagwarmaya da zai nemi takarar shugaban kasar Najeriya a 2027. Hoto: @sowore
Source: Facebook

Sowore, wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar AAC a zaben 2023, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV.

“Na fito takara ne domin cin zabe” – Sowore

'Dan siyasar ya ce jam’iyyarsa ta AAC za ta gudanar da zaben fitar da gwani a mako mai zuwa, sai dai bai tabbatar ko shi kadai ne zai tsaya takara ko yana da abokin hamayya ba.

Sowore ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya lashe zaben domin samar wa ‘yan Najeriya tsarin shugabancin da ba su saba gani a kasar ba.

“Ina takara ne domin cin zabe,” in ji Sowore.

Ya kara da cewa:

“Dukkan jam’iyyun siyasa iri daya ne, amma ya kamata mutanen da suke da kyawawan manufofi da dabaru su samu damar cin zabe a Najeriya.”

A cewarsa, halin da Najeriya ke ciki a yanzu ya fi na shekarun baya muni, musamman ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Sowore ya kara da cewa:

“Lokaci ya sauya, kuma Najeriya na cikin matsala mafi girma fiye da baya."

Sowore ya soki tsofaffin shugabanni

'Dan gwagwarmayar ya ce manufofin shugabannin da suka mulki Najeriya ne suka jefa kasar cikin matsalolin talauci, rashin tsaro da wahalhalu.

“Dukkan mutanen da ku ka ambata su ne suka jefa Najeriya cikin talauci, rashin tsaro, bakin ciki da hawaye,” in ji Sowore.

Sowore ya tambayi ko ‘yan Najeriya za su ci gaba da zaben mutanen da suka dade suna mulki duk da matsalolin da kasar ke fuskanta?

“Shin kuna son Najeriya ta ci gaba da zaben wadannan mutanen ne domin mutane su kara shan wahala?”

- Omoyele Sowore.

Sowore ya ce yana da manufofin ceto Najeriya fiye da na Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan takara.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Omoyele Sowore, wanda zai nemi takarar shugaban kasa a 2027. Hoto: @officialABAT, @sowore
Source: Twitter

Neman shugabancin Najeriya karo na 3

Idan Sowore ya samu tikitin takara, zaben 2027 ne zai zama karo na uku da yake neman shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar AAC, in ji rahoton The Cable.

Tun daga shekarun baya, Sowore ya kasance daya daga cikin fitattun masu sukar gwamnati da manyan jam’iyyun siyasa kan matsalolin tattalin arziki da tsaro da Najeriya ke fama da su.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Ya dade yana bayyana kansa a matsayin wani madadi da Najeriya take bunkata, wanda zai kawo karshen dukkan matsalolin da ake fama da su a kasar.

'Obi zai yaudari 'yan Arewa' - Sowore

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Omoyole Sowore ya zargi Peter Obi da kokarin yi wa 'yan Arewa dadin baki yayin da zaben 2027 ke zuwa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon 'dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya bayyana cewa Arewa ce kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.

Haka kuma ya shaida wa jama'a cewa yana da wasu manyan tsare-tsare da zai aiwatar idan ya samu damar zama shugaban kasa da za su farfado da shiyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com