Bayan Sace Yayar Tsohon Minista, Ƴan Bindiga Sun Harbe Shugaban Jam'iyyar Adawa

Bayan Sace Yayar Tsohon Minista, Ƴan Bindiga Sun Harbe Shugaban Jam'iyyar Adawa

  • 'Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar adawa a Osun yayin da jihar ke fama da hare-haren yan ta'adda
  • Majiyoyi suka ce an kai shi asibiti domin ba shi kulawa, kuma likitoci sun tabbatar yana samun sauƙi sosai
  • Rundunar 'yan sanda ta ce mahara biyu ne suka kai harin a kan babur yayin jami'ai suka fara farautar wadanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun sake kai hari a jihar Oyo inda ya rutsa da ɗan siyasa.

An tabbatar da cewa yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar Accord mai adawa, Asimiyu Ajibola.

An harbe shugaban jam'iyyar Accord a Oyo
Shugaban jam'iyyar Accord a Oyo, Asimiyu Ajibola da Sufeta-janar na ƴan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Comrade Nuru, Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rahoton Tribune ya tabbatar da cewa dan siyasar yana karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Osun.

Yadda aka harbe shugaban jam'iyyar Accord a Oyo

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar 'yan sanda na Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce rundunar ta fara gudanar da cikakken bincike kan harin harbin.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na dare, lokacin da wasu mutane biyu dauke da makamai a kan babur suka bude masa wuta.

Bayan samun rahoton gaggawa, rundunar 'yan sanda ta tura jami'an tsaro na musamman da na yau da kullum zuwa wurin domin daukar matakan gaggawa.

Jami'an 'yan sanda sun yi gaggawar kai Ajibola wani asibiti domin kula da lafiyarsa, inda yake ci gaba da samun magani a halin yanzu.

Ma'aikatan lafiya sun tabbatar da cewa Ajibola yana cikin kwanciyar hankali, kuma yana amsar magani yadda ya kamata bayan harin da aka kai masa.

Yan bindiga sun kai hari kan shugaban jam'iyyar adawa a Oyo
Taswirar jihar Oyo da ke fama da hare-hare a kwanakin nan. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakin da ƴan sanda suka dauka

Rundunar ta ce jami'anta sun fara farautarsu domin gano wadanda suka tsere, tare da tabbatar da cafke su da gurfanar da su gaban kotu.

A cewar sanarwar, binciken farko da aka gudanar a wurin ya sa an gano wasu kayayyaki da ake ci gaba da yi masu binciken kimiyya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban APC, sun masa bidiyo yana neman agaji

Ojelabi ya ce kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Gotan, ya yi Allah wadai da harin tare da bayar da umarnin kafa kwamitin bincike mai karfi.

Ya umurci dukkan sassan bincike su yi amfani da dukkan hanyoyin da ake da su domin gano musabbabin harin da kuma wadanda suka aikata shi.

Rundunar ta tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen binciken, tare da rokon jama'a su ba da sahihan bayanai.

Yadda ƴan bindiga suka addabi Kudu maso Yamma

Lamarin ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan karuwar hare-haren yan bindiga a wasu sassan yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Haka kuma, ranar Talata rundunar 'yan sandan Oyo ta bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin fasfo na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya da ke Ogbomoso.

Maharan sun gudu da bindiga, harsasai da wasu kayayyaki masu muhimmanci bayan harin da suka kai wa ofishin gwamnati.

'Yan bindiga sun sace yayar tsohon minista

A wani labarin, an ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da yayar tsohon Ministan makamashi a Najeriya tare da tagwayen ‘ya ’yanta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalibai a jihar Zamfara ana jimamin abin da ya faru a Oyo

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki lokacin da take kai ‘ya ’yanta makaranta, inda suka tafi da su da karfi.

Iyalan Bayo Adelabu sun tabbatar da lamarin, sun nemi addu’a da taimakon jama’a, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.