PDP Na Shirin Karfafa Damar Pantami Ta Zama Gwamna, Ta Fara Zawarcin Babban Jigo a APC

PDP Na Shirin Karfafa Damar Pantami Ta Zama Gwamna, Ta Fara Zawarcin Babban Jigo a APC

  • Ana matsa wa tsohon gwamnan Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya fice daga APC zuwa PDP domin mara wa Ali Isa Pantami baya a zaben 2027
  • Tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da Pantami na kokarin ganin Goje ya koma PDP bayan APC ta kasa ba shi tikitin takara
  • Majiyoyi sun ce tattaunawa na gudana tsakanin Goje da PDP kan yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Ana matsa wa tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Ana zawarcin Goje ne daga APC zuwa PDP domin mara wa dan takarar gwamnan jam’iyyar, Farfesa Ali Isa Pantami, baya a zaben 2027.

PDP na zawarcin Danjuma Goje
Sanata Danjuma Goje na jam'iyyar APC Hoto: Danjuma Goje
Source: Facebook

Majiyoyin Daily Trust sun ce tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da dan takarar gwamnan PDP na matsa wa Goje lamba ya koma jam’iyyar tun bayan da ya bayyana cewa APC ba za ta ba shi tikitin takarar sanata ba.

Kara karanta wannan

ADC ta kasa sasanta rikicinta a Katsina, manyan jiga jigai 2 sun fice daga cikinta

Mambobin PDP na ganin cewa komawar magoya bayan Goje da abokan siyasarsa daga kananan hukumomi da shiyyoyin sanata uku na jihar zuwa PDP za ta kara wa jam’iyyar karfi tare da bude hanyar samun nasarar Farfesa Pantami a watan Fabrairun 2027.

APC ta yi watsi da Goje

Goje, wanda ya kasance sanatan mazabar Gombe ta Tsakiya tun 2011 bayan ya kammala wa’adinsa biyu a matsayin gwamnan jihar, bai yi nasara a zaben fidda gwani da APC ta gudanar domin mazabar Gombe ta Tsakiya ba.

Tsohon gwamnan, wanda ya taba samar da gwamnoni biyu a jihar, yana da dimbin magoya baya a dukkan shiyyoyin sanata uku na Gombe.

Yunkurinsa na komawa majalisar dattawa a karo na biyar ya samu koma baya bayan kwamitin APC da ke kula da zaben fidda gwani na majalisar wakilai da dattawa a Gombe ya ayyana DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya) a matsayin wanda ya lashe tikitin mazabar Gombe ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Ba saban ba: Shugaban APC ya cire adawa, ya yaba wa ƴan PDP kan ƙoƙarinsu

Sai dai bayan da ba a ga sunansa cikin jerin ’yan takarar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar ranar Asabar da ta gabata ba, an ce Goje na tunanin komawa PDP domin ci gaba da rike kujerarsa a majalisa.

PDP da ADC na zawarcin Goje

An ce PDP da African Democratic Congress (ADC) na neman ganin Goje, wanda ake kallonsa a matsayin uban siyasar kusan dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar, ya koma cikinsu domin kara musu karfi gabanin babban zaben 2027.

Sai dai wasu majiyoyi daga bangaren Goje, wadanda suka nemi a boye sunayensu, sun bayyana cewa tattaunawa na gudana tsakanin tsohon gwamnan da PDP kan yiwuwar sauya shekar tasa zuwa jam’iyyar.

Goje na da tasiri a siyasar Gombe

Goje na daga cikin wadanda suka kafa PDP a shekarar 1998. Ya taba zama karamin ministan wutar lantarki da karafa a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a wa’adinsa na farko.

Daga bisani ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Gombe karkashin PDP. Ya koma APC a shekarar 2014, inda ya taimaka wa jam’iyyar wajen kwace mulki daga PDP a shekarar 2019.

Sai dai daga baya alakar siyasa tsakaninsa da uban siyasarsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta yi tsami, lamarin da ya kai ga kayar da Goje a zaben fidda gwani na APC da aka gudanar a watan Mayun da ya gabata.

Kara karanta wannan

PDP ta goyi bayan gwamnan Kebbi da ke APC domin tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Ana zawarcin Danjuma Goje a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

PDP ta yi kamu a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta yi babban kamu bayan karbar sakataren ADC yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar.

Sakataren jam'iyyar ADC na ƙaramar hukumar Gombe, Hon. Babangida Usman, wanda aka fi sani da Babangida Ventures, ya yi murabus daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng