An Yi Sabon Zaman Tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka a Birnin Washington DC

An Yi Sabon Zaman Tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka a Birnin Washington DC

  • Tawagar kasashen Najeriya da Amurka sun fara sabon zagaye na tattaunawa kan batun tsaro da yaki da ta’addanci
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya jagoranci tawagar Najeriya yayin da Allison Houker ta jagoranci tawagar Amurka
  • Kasashen biyu za su tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwar tsaro da yaki da ta’addanci a wannan taro a Washington DC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Tawagar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka ta fara sabon zagaye na tattaunawa a birnin Washington DC, inda batutuwan tsaro da yaki da ta’addanci suka kasance cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa a kai.

Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa kasar Smurka domin halartar taron da aka gudanar ranar Laraba.

Nuhu Ribdu
Mai ba shugaban Najeriya kan tsaro, Nuhu Ribadu tare da mataimakiyar ministan harkokin wajen Amurka Hoto: Rasheed_Adinoyi
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Amurka, Allison Houker, ta jagoranci tawagar Amurka a taron.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Manyan jami’an Najeriya sun halarci taron

Daga cikin jami’an Najeriya da suka halarci taron akwai Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Ministan Tsaro, Christopher Musa.

Haka kuma Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, na cikin jami’an Najeriya da suka halarci tattaunawar.

Abubuwan da aka tattauna a taron

Bisa tsarin ajandar taron, jami’an kasashen biyu za su tattauna kokarin da ake yi wajen yaki da ta’addanci, ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu da kuma matakan da ya kamata a dauka domin kara karfafa alakar Najeriya da Amurka.

Haka kuma an shirya gudanar da wani taron hadin gwiwa kan harkokin tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ranar Alhamis.

Yadda aka kafa tawagar hadin gwiwar

An kafa tawagar hadin gwiwar ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargi da tauye yancin addini.

Najeriya da Amurka sun gudanar da taron farko a Abuja a watan Janairu, a wani bangare na kokarin kara zurfafa hadin gwiwa kan harkokin tsaro da sauran batutuwan da kasashen biyu ke da muradin bai daya.

Kara karanta wannan

Yadda za a sabunta fadar sarkin Gombe ta zama ta yi zarra a Arewa

Kasashen biyu sun jaddada kare hakki

Gwamnatocin Najeriya da Amurka sun sake jaddada kudurinsu na kare 'yancin addini da kuma inganta muhimman hakkokin dan Adam a Najeriya.

Wadannan hakkoki sun hada da 'yancin fadin albarkacin baki, yin taro cikin lumana da kuma 'yancin addini ko yin imani da abin da mutum ya zaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262