An Shiga Rudani bayan Dan Wasan Katsina United da Aka Ce Ya Mutu Ya Farfado a Dakin Gawa
- Ozor Chinedu, dan wasan baya na kungiyar Katsina United, ya fadi a lokacin wasan sada zumunta da Niger Tornadoes a Katsina ranar Talata
- Likitoci sun bayyana dan wasan mai shekara 18 a matsayin wanda ya mutu, inda daga baya ma’aikatan dakin ajiye gawarwaki suka lura da motsi a jikinsa
- A halin yanzu Chinedu na cikin mawuyacin hali a babban asibitin Katsina, yayin da ake jiran rahoton likitoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - An shiga rudani kan halin da Ozor Chinedu, dan wasan baya na kungiyar Katsina United, ke ciki.
Rudanin ya samu ne bayan dan wasan ya fadi a lokacin wasan sada zumunta da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina ranar Talata, 11 ga watan Agustan 2026.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce dan wasan mai shekara 18, wanda Katsina United ta sayo kwanan nan daga Kano Pillars, ya fadi a fili yayin wasan gasar Gusau/Ahlan Pre-season Cup, inda aka garzaya da shi Asibitin K-Dara Specialist.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban ƙasa a Najeriya ya mutu yana cikin saduwa da wata mata? Gaskiya ta fito
Dan wasan Katsina United ya farfado
A cewar rahotanni, likitoci a asibitin sun bayyana cewa dan wasan ya mutu ya bar duniya bayan an kai shi asibiti.
Daga bisani, Katsina United ta fitar da sakon jaje, yayin da kungiyoyi da suka hada da Heartland da Kano Pillars suka yi jimamin dan wasan a shafukan sada zumunta.
Gwamnatin jihar Katsina ma ta shiga sahun masu aikawa da ta'aziyyar rasuwar dan wansan na kungiyar Katsina United, bayan samun labarin mutuwar.
Sai dai daga baya lamarin ya dauki sabon salo bayan ma’aikatan dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Janar na Katsina suka lura da motsi a jikin Chinedu.
An garzaya da shi sashen kulawa na musamman
Nan take aka mayar da shi Sashen Kulawa na Musamman (ICU), inda aka sanya masa iskar numfashi domin kokarin ceto raryuwarsa.
Jami’in yada labarai na kungiyar Katsina United, Nasir Gide, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an taba bayyana Chinedu a matsayin wanda ya mutu sau biyu kafin daga bisani aka gano alamun rai a tattare da shi.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau
Hakazalika, ita ma kungiyar Heartland FC, daya daga cikin tsofaffin kungiyoyin Chinedu, ta tabbatar da lamarin tare da rokon magoya bayansa su yi masa addu’ar samun sauki.
Ya zuwa safiyar ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026 Chinedu na cikin mawuyacin hali a babban asibitin Katsina, yayin da al’ummar kwallon kafa ke jiran rahoton likitoci kan makomar rayuwarsa.

Source: Original
Brighton ta sayi dan wasan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar ƙwallon ƙafa da ke wasa a gasar Premier League ta ƙasar Ingila, Brighton & Hove Albion, ta sayi matashin dan wasan Najeriya, Zadok Yohanna.
Kungiyar Brighton & Hove Albion ta dai kashe fam miliyan £21.5 wajen sayen matashin ɗan wasan gaba na Najeriya, Zadok Yohanna, daga ƙungiyar AIK Stockholm.
Ɗan wasan mai shekaru 18 wanda ke taka leda a ɓangaren hagu ko dama ya kuma zama matashi ɗan Najeriya mafi tsada.
Asali: Legit.ng