Bayan Shekaru 10 Ana tare kuma Ta Haifi ‘Ya ‘ya 3 Ronaldo Ya Auri Sahibarsa
- Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez sun daura auren sirri a garin Cascais na kasar Portugal
- Ma'auratan sun shafe shekaru kusan 10 suna tare tun bayan zamansu a birnin Madrid a kasar Sifen
- Sun bayyana labarin auren nasu ne ta hanyar wallafa hoton zobbansu a shafinsu na Instagram
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Portugal - Cristiano Ronaldo ya angwance da tsohuwar budurwarsa Georgina Rodriguez a wani taron sirri a kasar Portugal.
Fitattun masoyan sun kasance sun shafe shekaru kusan 10 sun tare kuma sun shaku, har an samu rabon ‘ya ‘ya da-dama a tsakaninsu.

Source: UGC
Cristiano Ronaldo ya auri Georgina Rodriguez
An samu labarin auren ne a wani hoto da Cristiano Ronaldo ya wallafa a dandalin Instagram ranar Talata 11 ga watan Agusta 2026.
Ronaldo mai shekaru 41 a duniya ya ambaci Georgina Rodriguez a wallafar da ya yi a shafinsa, hakan ya tabbatar wa kowa ita ya aura.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban ƙasa a Najeriya ya mutu yana cikin saduwa da wata mata? Gaskiya ta fito
Tun a shekarar 2016 lokacin yana kwallo a Real Madrid, Mista Ronaldo ya hadu da Rodriguez, a sa'ilin tana zaman wani shagon Gucci.
Bayan wadannan shekaru ana ta soyayya, har ta haifi ‘ya ‘ya biyar kuma tana kula da dayan yaron shi, ‘dan kwallon ya sa mata zobe.
Wace ce Georgina Rodriguez?
Rodriguez mai shekaru 32 da haihuwa ‘yar kasuwa ce wanda yanzu ta shahara a duniya.
Mahaifinta mai suna Jorge Rodriguez ‘dan kasar Argentina ne, ita kuma mahaifiyarta asalinta ‘yar Sifen ce wanda kusan ita ta rike ta.
Shekara guda cif da suka wuce ta bayyana cewa sun yi baiko da Ronaldo wanda ya buga kwallo a Ingila, Sifen, Italiya da Saudi a yanzu.
Haihuwa da 'ya 'yanta da Ronaldo
A karshen 2017 Rodriguez ta haifi diyar farko da Ronaldo sai kuma a Afrilun 2022 ta haifi tagwaye - amma namijin ya rasu wajen haihuwa.
Baya ga ‘ya ‘yan da ta haifa, ‘yar kasuwar ce ta ke kula da sauran yaran Ronaldo; babban ‘dan shi mai shekara 16 da wasu tagwayen.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau
Rahoton Sky Sports ya ce an daura wannan aure ne a Cascais, wani birni da ke da nisan mil 20 yamma da babban birnin kasar Portugal.
‘Ya ‘yan dan wasan biyar sun halarci wannan biki na musamman da aka yi a asirce a mahaifarsa.
Zuwa safiyar Laraba, mutane kusan miliyan 20 suka nuna sha’awarsu da labarin a Instagram, wasu 800, 000 sun tofa albarkacin bakinsu.
Adadin wadanda suka sake wallafa labarin wannan aure da aka daura kuwa sun zarce 600, 000 kamar yadda Legit Hausa ta lura dazu.
Rade-radin auren Ronaldo da Georgina
Tun a 2017 ake jin cewa Cristiano Ronaldo na shirin auren budurwarsa Georgina Rodriguez bayan ya ba ta zobe mai matuƙar tsada.
A lokacin, rahotanni sun nuna cewa an shirya gudanar da auren ne a shekarar 2018, ko da yake ba a bayyana takamaiman ranar biki ba.
Ronaldo ya sha nanata cewa yana fatan za su gudanar da gagarumin biki a nan gaba tare da iyalansa da sauran abokan arziƙi.
Asali: Legit.ng