Kwankwaso Ya San Matsayinsa da Peter Obi Ya Ayyana Abokin Takararsa na Zaben 2027
- Peter Obi ya ayyana tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa bayan samun tikitin shugaban kasa na NDC
- Dan takarar shugaban kasar ya yi alkawarin bunkasa tsaro, tattalin arziki da samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki cikin shekaru hudu
- Obi ya ce Najeriya na fuskantar kalubale masu yawa, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a iya ceto kasar ta hanyar samar da shugabanci nagari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ayyana tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya bayyana hakan ne yayin jawabin karbar tikitin takarar shugaban kasa da ya gabatar bayan tabbatar da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a wani babban taro na musamman da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.

Source: Twitter
Obi ya zabi Kwankwaso matsayin abokin takara
Da yake bayani kan dalilin zabar Kwankwaso, Obi ya ce tsohon gwamnan Kano mutum ne da ya yi fice wajen inganta ilimi da tsaro, in ji rahoton Leadership.
"Kwankwaso ya yi imani da ilimi. Ya yi imani da tsaro, kuma za mu yi aiki tare domin tabbatar da wadannan abubuwa sun samu," in ji Obi.
Nadin Obi ya biyo bayan fitowarsa a matsayin dan takara daya tilo da ya nemi tikitin shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben fidda gwani da aka gudanar ranar Juma'a, 29 ga Mayun 2026.
Jagoran NDC kuma tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, tare da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, suka mika tutar jam’iyyar ga Obi a hukumance.
Yayin da yake jawabin nuna godiya kan nasarar da ya samu, Peter Obi ya ayyana Kwankwaso a matsayin wanda yake so su mulki Najeriya tare idan sun ci zaben 2027.
Obi ya gabatar da sababbin manufofi
A jawabin da ya gabatar bayan karbar tikitin, Obi ya bayyana wasu muhimman manufofi da ya ce za su taimaka wajen fitar da Najeriya daga halin da take ciki.
Daya daga cikin manyan alkawurran da ya dauka shi ne samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki cikin shekaru hudu idan aka zabe shi shugaban kasa.
Ya kuma yi alkawarin magance matsalolin tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma rage gibin da ake samu a bangaren samar da ababen more rayuwa.
Najeriya na bukatar sabuwar hanya
Obi ya ce Najeriya na cikin wani mawuyacin hali da ya hada da matsalolin tsaro, durkushewar tattalin arziki da kuma rashin amincewar jama'a da gwamnati.
A cewarsa, matsalolin sun jefa 'yan kasa da kamfanoni cikin mawuyacin hali, amma har yanzu akwai damar ceto kasar idan aka samu shugabanci mai nagarta.
Asali: Legit.ng

