Za a Buga Siyasa a Kaduna, Isa Ashiru Ya Kafa Kwamitin Yakin Neman Zabe

Za a Buga Siyasa a Kaduna, Isa Ashiru Ya Kafa Kwamitin Yakin Neman Zabe

  • Hon. Isa Ashiru Kudan, ɗan takarar gwamnan Kaduna na ADC, ya naɗa shugabannin yaƙin neman zaɓensa na 2027
  • John Markus Ayuba ne aka naɗa Darakta-Janar, yayin da Bashir Ibrahim Sakadadi zai zama mataimakinsa
  • An kuma naɗa Abdulwaheed Olayinka Adubi a matsayin kakakin yaƙin neman zaɓen da sauran wasu mukamai a kwamitin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Isa Ashiru Kudan, ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya amince da naɗa wasu muhimman mutane a ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa gabanin zaɓen gwamna na 2027.

A cikin wata sanarwa da Ashiru Kudan ya fitar ranar Talata, ya naɗa John Markus Ayuba a matsayin Darakta-Janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen.

Kudan ya zabi shugaban kwamitin kamfe
Isa Ashiru Kudan tare da Malam Nasir El-Rufai Hoto: @IsaAshiruKudan
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Isa Ashiru ya kuma nada Hon. Bashir Ibrahim Sakadadi a matsayin mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben.

Kara karanta wannan

Kwana 3 kafin zabe, INEC ta ƙara sunan ɗan takara 1 a zaben gwamnan jihar Osun

Haka kuma, Ashiru Kudan ya naɗa Mukhtar Lawal Baloni a matsayin sakataren ƙungiyar, yayin da Abdulwaheed Olayinka Adubi, ɗan jaridar da ke zaune a Kaduna, zai zama kakakin yaƙin neman zaɓen.

Shirye-shiryen zaɓen 2027

Sanarwar ta ce an yi naɗe-naɗen ne domin ƙarfafa shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen gwamna na 2027 a jihar Kaduna, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Ta ƙara da cewa naɗe-naɗen sun nuna ƙudurin Ashiru na gina tsarin yaƙin neman zaɓe da zai haɗa kowa kuma ya mayar da hankali kan samun sakamako.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce naɗe-naɗen za su taimaka wajen ƙara faɗaɗa wayar da kan jama’a a matakin ƙasa da kuma inganta haɗin gwiwa a tsakanin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Bulus Yohanna, jami’in kula da harkokin ladabi; Mallam Ali Musa, mai ba da shawara na musamman kan sabbin kafafen yaɗa labarai; Hon. Auwal B.Z, mataimaki kan sabbin kafafen yaɗa labarai (Facebook); da Salim Tahiris, wanda zai zama mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yaɗa labarai (Facebook) da kuma mataimaki na kai tsaye.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi? An tsage gaskiya

Ayuba ya riƙe manyan mukamai

Ayuba, wanda masani ne, ma’aikacin banki kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, ana sa ran zai jagoranci dabarun yaƙin neman zaɓen bisa gogewarsa a harkokin mulkin gwamnati, banki da siyasa.

Ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanar da Kasuwanci daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda aka ayyana shi a matsayin ɗalibin da ya fi kowa samun maki a jarabawar tantancewa ta PhD.

Daga bisani ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kaduna a zamanin marigayi Gwamna Patrick Yakowa, sannan ya zama Kwamishinan Albarkatun Ruwa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Mukhtar Ramalan Yero.

Isa Ashiru Kudan ya kafa kwamitin kamfe
Hon. Isa Ashiru Kudan na jawabi a wajen taro Hoto: @IsaAshiruKudan
Source: Facebook

Ayuba ya kuma kasance mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna a zaɓen 2023. Yana da alaƙa da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Zangon Kataf da sauran sassan Kudancin Kaduna.

Ashiru ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa waɗanda aka naɗa za su yi amfani da gogewarsu a siyasa, ƙwarewar jagoranci da ƙudurin su wajen taimakawa ADC ta samu nasara a babban zaɓen 2027 da aka tsara gudanarwa a jihar.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka

Ashiru Kadan ya zabi abokin takara

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa, dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADC, Isa Ashiru Kudan, ya sanar da abokin takararsa a zaben 2027.

Isa Ashiru Kudan ya sanar da Barrista Irmiya Ishaku Kantiok a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng