Jam'iyyar PDP Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Atiku Ne Ya Ci Zabe

Jam'iyyar PDP Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Atiku Ne Ya Ci Zabe

  • Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu
  • PDP din dan takarar shugaban kasar ta ta shawarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta soke zaben shugaban kasar ta sake wani
  • Jam'iyyar ta PDP din ta bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta saba sashi na 65 na dokar zabe da wasu dokokin kasa yayin zaben

Jam'iyyar PDP a ranar Alhamis ta soki ayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban shugaban kasa na ranar Asabar, tana mai cewa dan takarar ta, Atiku Abubakar, shine ya lashe zaben.

Babban jam'iyyar hammayar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaranta na kasa, Hon. Debo Olagunaba, ya fitar.

Kara karanta wannan

A shirye muke: Peter Obi zai tafi kotu kan sakamakon zabe, APC ta yi martani mai zafi

Atiku da Tinubu
PDP Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Atiku Ne Ya Ci Zabe. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

The Punch ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ayyana Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas matsayin zababben shugaba bayan samun kuri'u 8,794,726 don cin zaben shugaban kasar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da wanda ya ci zaben a dakin tatattara sakamakon zabe na kasa da ke Abuja a safiyar ranar Laraba.

PDP ta umurci INEC ta kwace shaidar cin zabe da ta ba wa Tinubu

Babban jam'iyyar hamayyar, a ranar Alhamis ta bukaci hukumar zaben nan take ta karbe satifiket din cin zabe da ta ba wa Tinubu kuma ta soke zaben shugaban kasar.

Wannan bukatar, PDP din ta yi ikirarin, ya dace da sashi na 65 da Dokar Zabe na 2022.

A cewar babban jam'iyyar hamayyar, ayyana Tinubu matsayin wanda ya ci zabe, INEC ta saba tanade-tanade na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), dokar zabe na 2022 da dokokin da ka'idojin yin zaben shugaban kasa na 2023 ta INEC.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Amurka Ta Taya Tinubu Murna, Ta Ba Wa Sauran Yan Takara Shawara

Sanarwar ya ce:

"PDP ta yi imanin cewa dan takarar shugaban kasar ta, Atiku Abubakar, karara shine ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu saboda hujjar cewa shi ya samu halastattun kuri'u mafi rinjaye a akwatunan zabe.
"Abin bakin ciki, an tafka magudi da gangan da suka hada da kin amfani da na'urar BVAS da INEC ta yi, gaza tura sakamakon zabe zuwa matattara kai tsaye daga akwatunan zabe wanda ya saba wa sashi na 60 (4)(b) na Dokar zabe ta 2022.
"Wannan saba dokar zaben da INEC ta yi, wanda jam'iyyun siyasa, masu zabe, yan Najeriya daban-daban da masu saka ido kan zabe na gida da kasan waje, sun shaida cewa shi ya bada daman sauya sakamakon zabe da ba wa APC kuri'un."

Ta kara da cewa:

"Rashin dora sakamakon zaben kai tsaye daga akwatunan zabe da INEC ta yi, ya saba dokar zabe da dokoki da ka'idojinta, ya taba nagartar sakamakon zaben."

Kara karanta wannan

Ta tabbata: INEC ta ba Tinubu da Shettima shaidar su suka lashe zaben shugaban kasa

Don haka PDP ta ce saboda wannan dalilan ba zai yi wu a amince da sakamakon zaben ba.

Jam'iyyar ta PDP ta ce ita da dan takarar shugaban kasar ta sun fara daukan matakin zuwa kotu don kwato nasararsu a zaben shugaban kasa na 2023.

PDP ta yi kira ga magoya bayanta da yan Najeriya su zauna lafiya, kada su cire tsammani su jajirce wurin kare dimokradiyya da nasarar jam'iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Amurka ta taya Bola Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasar Najeriya

A wani rahoton kasar Amurka ta taya Bola Tinubu na jam'iyyar APC murnar lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Amurkan ta kuma yi kira ga yan Najeriya su kwantar da hankula sannan duk masu zargin magudi su tafi kotu su bi tsarin da doka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel