1448: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Shirin Shiga Watan Maulidin Annabi SAW

1448: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Shirin Shiga Watan Maulidin Annabi SAW

  • Majalisar Sarkin Musulmi ta jihar Sokoto ta fitar da sanarwa game da duban watan Maulidi a Najeriya
  • Majalisar ta bukaci Musulmi su lura da sararin sama, sannan su kai rahoton ganin wata ga shugaban gunduma ko ƙauye mafi kusa
  • Rahotannin ganin watan za a isar da su ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ta tsarin shugabancin gargajiya na ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Majalisar Sarkin Musulmi a jihar Sokoto ta fitar muhimmiyar sanarwa yayin da ake shirin shiga watan Maulidi da ake gudanarwa a kowace shekara.

Fadar ta sanar da Alhamis, 13 ga Agusta 2026, a matsayin ranar da Musulmi za su fara neman jinjirin watan Rabi’ul Awwal 1448AH.

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa game da duba jinjirin wata
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Sanarwar ta fito ne daga wata takarda da Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sultan, ya fitar ranar Laraba, 12 ga Agusta, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

PDP ta yi sabon ango, dan majalisa a Kano ya watsar da jam'iyyar Abba Kabir

Yaushe za a fara duba watan Rabi’ul Awwal?

A cewar sanarwar, 13 ga Agusta ya yi daidai da ranar 29 ga watan Safar 1448AH, don haka ita ce ranar da ta dace a fara neman jinjirin Rabi’ul Awwal.

Majalisar ta bukaci Musulmi su kula sosai da sararin sama domin neman sabon wata, sannan su gaggauta sanar da shugaban gunduma ko ƙauye mafi kusa idan sun tabbatar da ganinsa.

“Musulmi ana bukatar su fara neman sabon watan Rabiul Awwal 1448AH ranar Alhamis, sannan su kai rahoton ganin watan ga shugaban gunduma ko ƙauye mafi kusa."

- In ji sanarwar.

Majalisar ta bayyana cewa za a isar da rahotannin ganin watan ta hanyar shugabannin gargajiya zuwa ga Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar.

Sarkin Musulmi shi ne kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, wato NSCIA, wadda ke da alhakin daidaita manyan harkokin addinin Musulunci a ƙasar.

Kara karanta wannan

Sheikh Baffa Hotoro ya shiga babbar matsala kan taɓa mutuncin marigayi Dahiru Bauchi

Sarkin Musulmi ya ba yan Najeriya shawara
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Shawarar Sarkin Musulmi ga yan Najeriya

Majalisar ta yi kira ga Musulmi da su shiga aikin neman jinjirin watan, tana mai bayyana hakan a matsayin wani nauyi na addini, cewar Daily Post.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Allah Madaukakin Sarki Ya taimaka mana wajen sauke wannan nauyin addini, amin."

Wasu daga cikin yan Najeriya na gudanar da bikin Maulidi ne a kowane watan uku na Musulunci da aka fi sani da Rabi’ul Awwal domin bikin ranar haihuwar Manzon Allah SAW.

Gwamnatin Najeriya da na wasu jihohi na bayar da hutu musamman saboda wannan rana domin ba yan kasar damar gudanar da bukukuwa cikin kwanciyar hankali.

An kama mutane da makamai a bikin Maulidi

A baya, mun ba ku labarin cewa yan sanda sun cafke mutane 30 da ake zargi da aikata laifuffukan da suka shafi ta'addanci da daba a jihar Neja.

An kama wadannan mutanen ne a wuraren da musulmi suka taru suna bikin Maulidin Annabi Muhammad SAW a birnin Minna.

Kara karanta wannan

Yadda za a sabunta fadar sarkin Gombe ta zama ta yi zarra a Arewa

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Neja ya ce yanzu haka ana kan bincike, ya kuma bayyana makaman da aka kwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.