Jerin Gwamnoni 7 da Suka Samu Tikitin Takarar Sanata na Jam'iyyar APC a Zaben 2027
Abuja, Nigeria - A makon da ya gabata ne jam'iyyar APC ta gudanar da zabukan fitar da gwani na 'yan takarar Majalisar dattawa da Majalisar wakilan tarayya a duka jihohin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
APC ta yi amfani da tsarin masalaha wajen fitar da yan takararta na sanata, sai dai daga bisani ta shirya zabe a mazabun da aka samu rikici tsakanin masu neman takara.
A wani rahoto da The Cable ta atattaro, gwamnoni da dama da wa'adinsu zai kare a shekarar 2027 sun nemi takarar sanata domin a ci gaba d damawa da su a harkokin mulki.
Rahotanni sun nuna cewa sanatoci 51 masu ci sun samu tikitin sake tsayawa takara a APC yayin da wasu sanatoci 14 suka sha kaye a zaben fitar da gwani da aka gudanar
Legit Hausa ta tattaro muku gwamnoni bakwai masu ci da suka samu tikitin takarar Sanata na jam'iyyar APC mai mulki. Ga su kamar haka:
1. Gwamna Abdullahi Sule
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya samu tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Nasarawa ta Arewa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An bayyana sakamakon ne a garin Akwanga, hedikwatar mazabar sanatan, ta bakin shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC a jihar, Musa Shuaibu Guri.

Source: Facebook
Guri ya ce Gwamna Sule ya samu kuri’u 45,393 inda ya doke abokin takararsa, tsohon mataimakin gwamna kuma tsohon Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyukan Yi (NDE), Silas Ali Agara, wanda ya samu kuri’u 2,915.
"Gwamna Sule ya cika duk sharudan kundin tsarin mulkin APC da dokokin zabe, sakamakon ya samu mafi yawan kuri’u, na ayyana shi a matsayin dan takarar Sanatan Nasarawa ta Arewa," in ji shi.
2. Gwamna Inuwa Yahaya
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya zama ɗan takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Gombe ta Arewa bayan samun gagarumar nasara a zaɓen fitar da gwani.

Kara karanta wannan
Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki
Tashar Channels tv ta ruwaito cewa gwamnan ya bi layin da mambobin APC suka yi don kada kuri'a a lokacin zaben, wanda ya gudana a mazabu 52.

Source: Facebook
Da yake jawabi bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada ƙudirin ci gaba da aikin raya Jihar Gombe da kuma tabbatar da manufofin APC a yankin.
3. Gwamna Hope Uzodimma
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya samu tikitin zama ɗan takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Imo ta Yamma bayan samun kuri’u 230,464 a zaben fitar da gwani.
Gwamna Uzodimma ya kayar da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, wanda ya samu kuri’u 1,098 kacal a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 12 na mazabar sanatan.
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanim APC na majalisar tarayya a jihar Imo, Williams Kayoda, ne ya bayyana sakamakon a hedikwatar ƙaramar hukumar Orlu, cewar rahoton Premium Times.

Source: Facebook
4. Gwamna Dapo Abiodun
Gwamna Dapo Abiodun na cikin jerin gwamnonin APC da suka samu tikitin takarar sanata a zaben 2027 bayan nasarar da ya samu a zaben fitar da gwani na mazabar Ogun ta Gabas.

Kara karanta wannan
Atiku ya lallasa yan takara 2, ya samu nasara a zaben fitar da gwanin ADC a Sakkwato
This Day ta rahoto cewa Aboidun ya samu nasarar ne bayan lallasa Sanata mai ci, Gbenga Daniel, wanda ya janye daga takara awanni kadan kafin fara zaben fitar da gwanin APC.

Source: Twitter
5. Gwamna Ahmadu Fintiri
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya lashe tikitin jam'iyyar APC na talarar Sanatan Adamawa ta Arewa ba tare da hamayya ba, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
Kamar abin da ya faru a Ogun, Gwamna Fintiri ya samu tikitin jam’iyyar APC ne bayan da Sanata mai ci, Amos Yohanna, ya sanar da cewa ba zai sake neman tsayawa takara a karo na biyu ba.

Source: Twitter
6. Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya samu tikitin takarar Sanatan Kwara ta Tsakiya a zaben fitar da gwanin da aka gudanar mai cike da rudani.
An samu rudani ne bayan sunan Sanata mai ci, Saliu Mustapha ya bayyana a cikin jerin sunayen masu neman takara da APC ta amince su gwabza a zaben gwani na Kwara ta Tsakiya.

Source: Twitter
Sanata Mustapha dai na cikin wadanda suka nuna sha'awar neman takarar gwamnan jihar Kwara a zaben 2027, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
7. Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya samu tikitin zama dan takarar Sanata na jam'iyyar APC a mazabar Yobe ta Gabas.
Gwamna Buni wanda zai fara zuwa wakilci a majalisar dattawa a karon farko shi ne 'dan takarar jam’iyyar daya tilo bayan da Sanata mai ci, Musa Mustapha ya janye masa.
The Nation ta ce masu ruwa da tsakin APC a mazabar Yobe ta Gabas sun tabbatar da Gwamna Buni a matsayin dan takarar sanata a taron da aka gudanar ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026.

Source: Facebook
APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi, ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a jihar.
Danladi ya kayar da sauran masu neman takara 14, ciki har da wani sanata mai ci, a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 16 na jihar Kwara.
Zaɓen fitar da gwanin ya biyo bayan kwanaki na takun-saka da lissafin siyasa a cikin jam’iyya mai mulki kan wanda zai gaji GwamnanAbdulRahman AbdulRazaq.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
