APC Ta Yarje wa Yahaya Bello da Wasu Su Nemi Takarar Kujerar Sanata a 2027

APC Ta Yarje wa Yahaya Bello da Wasu Su Nemi Takarar Kujerar Sanata a 2027

  • Yahaya Bello da Sanata Sunday Karimi na cikin ’yan takarar da kwamitin tantance APC ya amince su fafata a zaɓen fidda gwani na sanatoci a Kogi
  • Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, zai kara da Momoh Yusuf Obaro da Ibrahim Yakubu Adoke domin neman tikitin APC na Kogi ta Tsakiya
  • Jam’iyyar PDP ta fitar da ’yan takarar majalisar wakilai ta hanyar maslaha a wasu mazaɓu, yayin da tsofaffin ’yan majalisa suka samu tikiti a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lokoja, Kogi - Tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello da Sanata Sunday Karimi za su tsaya takara a zaben 2027.

Karimi mai wakiltar Kogi ta Yamma da Yahaya Bello na cikin ’yan takarar da kwamitin tantance APC ya amince da su.

APC ta tantance Yahaya Bello a Kogi
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello. Hoto: Alhaji Yahaya Bello.
Source: Facebook

An tantance Yahaya Bello domin takarar sanata

Kara karanta wannan

2027: Mijin Laila, Yusuf Gagdi ya rasa tikitin komawa majalisar wakilai a APC

Kwamitin tantance ’yan takarar APC ya amince da ’yan takarar sanatoci 17 daga yankunan sanatoci uku na jihar domin zaɓen fidda gwani ranar Litinin, cewar Punch.

An tabbatar da cancantar Yahaya Bello bayan an sanya sunansa a matsayi na 13 cikin jerin ’yan takarar da aka tantance domin Kogi ta Tsakiya.

Ana sa ran tsohon gwamnan zai fafata da Momoh Yusuf Obaro da Ibrahim Yakubu Adoke domin samun tikitin APC na yankin Kogi ta Tsakiya.

A Kogi ta Yamma kuwa, Sanata Sunday Karimi ya zama ɗan takarar maslaha bayan taron masu ruwa da tsaki ƙarƙashin jagorancin gwamna Usman Ododo.

Ko da yake an tantance wasu mutum shida ciki har da tsohon Sanata Smart Adeyemi da Aro Bamidele, ana ganin Karimi ne ke gaba.

Yahaya Bello zai gwabza da Sanata Natasha
Taswirar jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan takara da aka tantance a Kogi ta Gabas

A Kogi ta Gabas, APC ta tantance mutum bakwai domin fafatawa a zaɓen fidda gwani, ciki har da Sanata Isah Echocho da Joseph Ameh.

A gefe guda kuma, jam’iyyar PDP ta fitar da ’yan takarar majalisar wakilai a Kogi ta hanyar maslaha a wasu mazaɓun tarayya daban-daban.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

Tsohon ɗan majalisa Abdulrahman Badamasuiy ya zama ɗan takarar PDP na mazaɓar Okehi/Adavi bayan ya wakilci yankin tsakanin 2011 zuwa 2015.

Haka kuma, Mohammed A. Etudaiye ya samu tikitin Okene/Ogori-Magongo, yayin da Lawal Idrisu ya zama ɗan takarar Ajaokuta Federal Constituency.

A Kogi ta Yamma, Abdulkadir Ibrahim ya samu tikitin Lokoja/Kogi, yayin da Femi Victor Olubiyi ya zama ɗan takarar Kabba/Bunu Federal Constituency.

Ibigbemi Seun Samuel ya samu tikitin Yagba ba tare da hamayya ba, yayin da Abubakar Yahaya ya samu tikitin mazabar Ankpa/Olamaboro/Omala, cewar Daily Post.

Yahaya Bello zai nemi sanata a Kogi

An ji cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen 2027.

Ya sanar da wannan mataki ne a fadar Ohinoyin Ebira, inda manyan shugabannin gargajiya da addini suka nuna masa goyon baya.

Matakin nasa ya haifar da rade-radi game da fafatawa kai tsaye da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke rike da kujerar a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com