Farfesa Rabi'a daga Kano Ta Yi Magana kan Mukamin da Aka Nada ta a Majalisar Dinkin Duniya

Farfesa Rabi'a daga Kano Ta Yi Magana kan Mukamin da Aka Nada ta a Majalisar Dinkin Duniya

  • Malama a jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), FarfesaRabia Sa’id ta yi karin haske kan nadin da aka yi mata a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya
  • Martanin Farfesa Rabia na zuwa ne bayan labarin nadin da aka mata ya sake bulla a kafafen sada zumunta a Najeriya
  • Rahoto ya nuna cewa an nada ta a kwamitin da zai yi nazarin illolin zahiri da na zamantakewa na makamin nukiliya a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Farfesar Physics a Jami’ar Bayero Kano (BUK), Rabia Sa’id, ta bayyana cewa nadin da aka yi mata a Kwamitin Kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya kan Illolin Yaƙin Nukiliya (2025–2027) ba sabo ba ne.

Wannan kalamai na zuwa ne bayan labarin nadin da aka yi mata ya sake bulla a kafafen yada labarai daban-daban a Najeriya.

Kara karanta wannan

BUK: Mace 'yar jihar Kano ta yi zarra, ta samu muƙami a Majalisar ɗinkin duniya

Rabia Said.
Mamba a kwamitin Majalisar dinkin duniya kan illar nukiliya ga rayuwar dan adam, Farfesa Rabia Sa’id Hoto: Rabia Sa'id
Source: Facebook

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook da aka tabbatar, Farfesar ta ce Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya naɗa ta cikin kwamitin mutum 21 tun watan Disambar bara.

Nadin, wanda aka kafa bisa ƙudurin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 79/238, ya sanya Farfesa Rabia cikin manyan masana kimiyya da ke nazarin barazanar nukiliya da ka iya shafar rayuwar duniya.

Yadda aka sake yada nadin Farfesa Rabia

Wani rahoto da Premium Times ta wallafa bisa wani bayani daga BUK Media ranar Litinin ya sake jawo hankalin jama’a kan nadin nata.

Bayan wasu martani da aka samu a kafafen sada zumunta, Farfesa Rabia Sa'id ta bayyana cewa rahotannin ba sa nufin sabon nadi ' ne.

“Duk da cewa ina godiya da fatan alherinku, ya kamata a sani cewa wannan ba sabon nadi ba ne.
"Shi ne nadin da muka yi bikin sa a bara lokacin da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da mambobin Kwamitin da aka lafa kan illolin yaƙi da makamin nukiliya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

“Ina ganin wani ne kawai ya sake wallafa shi, sannan aka ci gaba da yadawa har ya bazu," in ji ta.

Kwamitin ya fara aiki tun Disamba

Rabia ta ce kwamitin ya fara gudanar da aikinsa ne tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan Disamban 2025 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

Ta bayyana cewa tun bayan kaddamar da kwamitin, mambobinsa sun gudanar da taruka ta yanar gizo da dama, sannan suka gudanar da wani taron kai tsaye a Vienna, Austria, a watan Maris.

Rabia Sa'id.
Farfess Rabia Sa’id ta jami'sr BUK da ke Kano tana tsskiyar aiki ofishinta. Hoto: Rabia Sa'id
Source: Facebook

Ta ce za a sake gudanar da wani taro a Geneva, Switzerland, a watan Satumba, tare da wasu tarurrukan tuntubar masu ruwa da tsaki a yankuna daban-daban kafin gabatar da rahoton ƙarshe a Taron Majalisar Dinkin Duniya a 2027.

An fara shirin zabe a Majalisar dinkin duniya

Kun ji cewa 'yan takara shida da ke neman kujerar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya sun fara gabatar da manufofinsu a wani taron tambayoyi da aka shirya.

Majalisar Dinkin Duniya dai na fuskantar matsananciyar matsalar kudi da kuma raguwar amincewar kasashe a duniya bayan zargin fa gwamnatin Amurka ta mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262