Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na Tsaka Mai Wuya, Jam'iyyar PDP Ta Yi Bayani

Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na Tsaka Mai Wuya, Jam'iyyar PDP Ta Yi Bayani

  • Jam'iyyar PDP ta yi karin haske kan danbarwar shari'a da ake yi kan sahihancin takarar Sheikh Isa Ali Pantami a jihar Gombe
  • PDP ta bayyan cewa tana jiran hukuncin kotu kan rikicin takarar gwamnan Gombe da ya shafi tsohon ministan sadarwa
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa babu wani rikicin takara a sauran jihohin bayan kammala zaben fitarda gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyya PDP ya yi bayani kan tsaida tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin dan takarar gwamnan Gombe a 2027.

PDP ta ce tana jiran hukuncin kotu domin kawo karshen rikicin da ya biyo bayan fitowar Sheikh Pantami, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Gombe.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa Pantami, wanda ya kasance mamba a jam'iyyar APC, ya sauya sheka zuwa PDP a watan Mayu kafin ya lashe tikitin takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Siyasar Gombe ta ɗauki zafi, dan takarar gwamna ya kai korafi ga ƴan sanda

Sai dai wasu jiga-jigan PDP da suka yi adawa da sauya shekar tasa da kuma nasararsa sun garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben fidda gwani.

PDP na fama da rikicin takara a jihohi?

Binciken da jaridar Nigerian Tribune ta gudanar ya nuna cewa, baya ga rikicin Gombe, PDP ta gudanar da zabukan fidda gwani cikin lumana a mafi yawan jihohi.

An bayyana cewa galibin 'yan takarar jam'iyyar, ciki har da dan takarar shugaban kasa, Sanata Sandy Onor, sun fito ne ta hanyar maslaha.

Mai magana da yawun PDP na kasa, Hon. Jungudo Haruna Mohammed, ya ce jam'iyyar ba ta da wata matsalar tikiti ko rikicin da zai bukaci kafa kwamitin sulhu.

Ya ce:

"Mun gudanar da sahihin tsari a dukkan jihohi. Wannan ita ce sabuwar PDP, ba mu maye gurbin sunan wanda ya yi nasara ba, kuma ba mu tilasta wa kowa janyewa ba."

An mika sunayen 'yan takara ga INEC

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan sayo motocin alfarma a kan N15.13bn

Jungudo ya bayyana cewa PDP ta riga ta mika sunayen 'yan takararta na shugaban kasa da na Majalisar Tarayya zuwa shafin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Ya ce:

"Mu ba APC ba ne. Ba mu sauya sunan kowa ba. Saboda haka ba mu da bukatar kwamitin sulhu, tsarinmu ya kasance cikin adalci da gaskiya."

PDP na jiran hukuncin kotu kan Pantami

Sai dai ya tabbatar da cewa har yanzu ana jiran hukuncin kotu kan shari'ar da ta shafi takarar Pantami a Gombe.

"A shari'ar Gombe, kotu ta dage hukunci. Muna jira. Bayan wannan, ba mu da wata matsala game da sakamakon zabukan fidda gwani," in ji shi.
PDP Nigeria.
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP Hoto: @officialPDPNig
Source: Facebook

Har ila yau, bangaren PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ya kuma fitar da Mohammed Yayari a matsayin dan takarar gwamnan Gombe.

An dora sunan Pantami a shafin INEC

Kun ji cewa Kungiyar Pantamiyya Movement ta sanar da cewa jam'iyyar PDP ta kammala tura bayanan takarar Farfesa Isa Ali Pantami zuwa shafin hukumar INEC.

A wata sanarwar manema labarai da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin kungiyar Pantamiyya, an ce an kammala aikin sanya bayanan ne a ranar 26 ga Yulin 2026.

Pantamiyya ta bayyana cewa hakan wata muhimmiyar nasara ce ga dimokuradiyya, tana mai nuna kwarin gwiwar samun shugabanci nagari a Gombe

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262