Pantami Na Shirin Sanin Makomarsa, PDP Ta Samu Koma Baya a Gombe

Pantami Na Shirin Sanin Makomarsa, PDP Ta Samu Koma Baya a Gombe

  • Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP guda biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar yayin da ake shirin zaben 2027
  • Tsohon shugaban karamar hukumar Funakaye, Ibrahim Yusuf, ya ce ya janye kansa daga PDP nan take
  • Mataimakin sakataren PDP a jihar Gombe, Mohammed Babani Bajoga, shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) guda biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar.

Ficewar tasu ta kara nuna yadda ake samun sauye-sauyen siyasa a jihar gabanin babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Wasu jiga-jigan PDP a Gombe sun fice daga jam'iyyar
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Prof Isa Ali Pantami
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon shugaban karamar hukumar Funakaye kuma tsohon shugaban PDP a karamar hukumar, Hon. Alhaji Ibrahim Yusuf, da mataimakin sakataren jam’iyyar a jihar Gombe, Hon. Mohammed Babani Bajoga, sun sanar da murabus dinsu a wasu wasiku daban-daban.

Kara karanta wannan

Ba Atiku ba Obi ba: 'Dan takarar shugaban kasa da ya cancanci 'yan adawa su tsaida a 2027

Ibrahim Yusuf ya bar PDP

A wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 2 ga watan Agusta, 2026, wadda ya aika wa shugaban PDP na mazabar Bajoga ta Yamma, Ibrahim Yusuf ya ce ya janye matsayinsa na zama mamba daga jam’iyyar nan take.

Ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan yin nazari sosai da kuma la’akari da wasu dalilai na kashin kansa.

Ibrahim Yusuf ya ce yana godiya da damar da jam’iyyar ta ba shi ta yin aiki a mukamai daban-daban, ciki har da shugabancin PDP a karamar hukumar Funakaye.

Tsohon shugaban karamar hukumar ya bukaci a cire sunansa daga kundin mambobin jam’iyyar da sauran bayanan hukuma.

“Ina godiya da goyon baya da hadin kan da na samu daga mambobi a tsawon shekarun da na yi ina aiki. Ina yi wa jam’iyyar da shugabanninta fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.”

Babani Bajoga ya yi murabus

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka nemi N80m bayan sace basarake

Hakazalika, Mohammed Babani Bajoga ya sanar da ficewarsa daga PDP a wata wasika mai dauke da ranar 3 ga watan Agusta, 2026.

Babani Bajoga ya aika wasikar ne ga shugaban PDP na mazabar Bajoga ta Gabas, inda ya ce ya janye daga matsayinsa na zama mamba daga jam’iyyar bisa radin kansa kuma nan take.

Tsohon mataimakin sakataren PDP a jihar Gombe ya ce ya yanke hukuncin ne bayan yin nazari sosai kan wasu batutuwan da suka shafe shi, yana mai cewa matakin nasa na karshe ne.

Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na rike mukamai daban-daban tare da yaba wa mambobinta kan goyon baya da hadin kan da suka ba shi a lokacin da yake kan mukaminsa.

Ba su bayyana dalilin ficewa ba

Sai dai babu daya daga cikin tsofaffin jami’an jam’iyyar biyu da ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar barin PDP.

Haka kuma, ba su bayyana jam’iyyar siyasar da za su koma ba bayan ficewarsu daga PDP mai adawa a jihar Gombe.

Jiga-jigan PDP a Gombe sun fice daga jam'iyyar
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dan takarar APC ya kai kara gaban IGP

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na tsaka mai wuya, jam'iyyar PDP ta yi bayani

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a Gombe, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya mika takardar koke ga Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya.

Jamilu Gwamna ya kai mika takardar koke ne kan zargin cin zarafi ta intanet, bata suna da kuma yada labaran karya gabanin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng