Rikicin APC Ya Kara Tsanani, Gwamna AbdulRazaq Ya Zabi Wanda Zai Gaje Shi a 2027

Rikicin APC Ya Kara Tsanani, Gwamna AbdulRazaq Ya Zabi Wanda Zai Gaje Shi a 2027

  • Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana wanda yake goyon bayan ya zama magajinsa a zaben da za a yi a farkon 2027
  • AbdulRazaq, wanda wa'adinsa na biyu zai kare a 2027, ya zabi Abdulfatai Yahaya Seriki a matsayin dan takarar gwamnan da yake goyon baya a APC
  • Wannan mataki da gwamnan ya dauka na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar APC ke fama da rikicin cikin gida tun bayan fara zabukan fitar da gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya ayyana Abdulfatai Yahaya Seriki a matsayin wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027.

Wannan matakin da Gwamna AbdulRazaq ya dauka na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rikicin siyasa a cikin jam’iyyar APC ta jihar Kwara.

Kara karanta wannan

"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

Gwamna.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulArazaq yana jawabi a wurin taro a Ilorin Hoto: @AARahman
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana Seriki a matsayin wanda yake fatan ya zama magajinsa a wata sanarwa da Gwamnatin Kwara ta fitar yau Talata, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Sanarwar ta fito ne kasa da sa’o’i 24 bayan ce-ce-ku-ce da rikice-rikice sun dabaibaye zaben fidda gwani na Sanatan Kwara ta Tsakiya, inda aka samu sabani kan matsayar Sanata Saliu Mustapha.

Rikicin APC ya kara tsananta a Kwara

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa matakin ya kara bayyana rikicin da ke tsakanin AbdulRazaq da Mustapha kan iko da kuma batun wanda APC za ta ba takarar gwamnan a 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, AbdulRazaq ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntubar shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya bayyana Yahaya Seriki a matsayin mutum mai kishin jama’a, hangen nesa da kuma kwarewar shugabanci.

“Na yanke shawarar bayyana Ambasada Abdulfatai Yahaya Seriki a matsayin wanda nake so ya zama magajina karkashin jam’iyyar APC,” in ji gwamnan.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi karin haske

Gwamnan ya ce goyon bayan da ya nuna wa Seriki ba yana nufin raina sauran masu neman takarar ba ne, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Ya bayyana cewa akwai masu neman takara gwamna kusan 16, amma mutum daya ne kawai zai samu damar tsayawa takara a karshe.

AbdulRazaq ya kuma bukaci shugabanni da mambobin APC su mara wa Seriki baya domin tabbatar da hadin kai da ci gaban jam’iyyar a jihar.

Sanata Mustapha.
Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha Hoto: Saliu Mustapha
Source: Facebook

Rikici tsakanin gwamna da Mustapha

Hakan na iya kara haddasa takun-saka tsakanin bangaren gwamnan da na Sanata Saliu Mustapha kafin zaben fitar da gwani na gwamna da za a gudanar ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

A cikin watannin baya-bayan nan, an dade ana alakanta bangarorin biyu da fafutukar kwace iko da APC ta jihar Kwara.

Bolarinwa ya fito takarar gwamnan Kwara

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kwara, Bashir Bolarinwa, ya ayyana kudirinsa na neman takarar gwamna a jihar a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Pantami ko Jamilu Gwamna: An ji wanda ya fi cancanta ya zama ɗan takarar APC a Gombe

Bashir Bolarinwa, ya bayyana cewa yana dakwarewa da hangen nesan da ake bukata wajen magance kalubalen tattalin arziki da shugabanci a jihar.

Ya bayyana cewa karatunsa na digiri na uku a fannin hulda da kasashen duniya, da karatu daga jami’o’i daban-daban, sun kara masa fahimtar shugabanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262