Bayan 'Yan Ta'adda Sun Kutsa Makaranta An Sace Dalibai, Gwamna Zulum Ya Dauki Mataki
- Gwamnatin Borno ta dauki mataki a kan makarantar da 'yan ta'adda suka kutsa wata makaranta tare da sace sace dalibai 42 a Askira/Uba
- An mayar da daliban makarantar zuwa Uba domin ci gaba da karatu bayan an tabbatar da cewa za a samar masu da tsaro a inda suka koma
- Iyaye sun roki gwamnati ta kara kaimi wajen kubutar da yaran da aka sace tare da dawo da su cikin yan uwa da iyayensu lami lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Borno - Gwamnatin jihar Borno ta sanar da rufe makarantar sakandare da ke Mussa a karamar hukumar Askira/Uba bayan harin da ake zargin ‘yan ta’adda sun kai, suka yi garkuwa da dalibai 42.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Dauda Illiya, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce kwamishinan ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na jihar, Lawan Wakilbe, ne ya sanar da matakin yayin wata ziyara da tawagar gwamnati ta kai yankin.
An rufe makarantar Borno da aka dauke dalibai
PM News ta ruwaito cewa sanarwar ta ce ziyarar na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka bayan aukuwar lamarin, tare da ci gaba da kokarin tabbatar da an ceto daliban cikin koshin lafiya.
Kafin Isa Mussa, tawagar ta kai gaisuwar ban girma ga Sarkin Uba, Alhaji Ali Ibn Ismaila Mamza II, a fadarsa da ke Uba.
A Mussa kuwa, jami’in rundunar soja ta bataliya ta 115 da ke Askira, Laftanar Kanal Ishola Olufisola, tare da shugabannin al’umma da iyayen yaran da aka sace ne suka tarbi tawagar.

Source: Twitter
Yayin wata ganawa da iyayen daliban, Wakilbe ya mika sakon jajantawa daga gwamnatin da al’ummar jihar Borno, yana mai tabbatar musu da cewa ana kara zage damtse domin ganin an kubutar da yaran cikin gaggawa.
Ya ce gwamnatin gwamna Babagana Umara Zulum na bai wa tsaron dalibai muhimmanci sosai a fadin jihar domin su samu ilimi a cikin nutsuwa.
An sauya wa daliban Borno makaranta
A matsayin matakin gaggawa, kwamishinan ya bayar da umarnin rufe makarantar ta Mussa na wucin gadi tare da mayar da ita zuwa makarantar sakandare da ke Uba a jihar Borno.
Ana sa ran daliban za su ci gaba da karatu a sabon wurin cikin yanayi mafi aminci da kariya, yayin da ake kokarin ceto 'yan uwansu da aka sace.
Da yake magana a madadin iyayen yaran, Ishaku Jidaye ya yabawa gwamna Zulum bisa saurin daukar mataki da nuna damuwa kan lamarin, tare da rokon gwamnati ta kara himma wajen ganin an sako yaran cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa iyalan yaran na cikin matsanancin damuwa da tashin hankali tun bayan faruwar lamarin. Tawagar gwamnatin ta kuma kai ziyara garuruwan Dille da Lassa domin duba halin tsaro da kuma tantance yanayin makarantu a yankunan da abin ya shafa.
Haka kuma, an duba wasu makarantu da ayyukan gine-gine domin tabbatar da cewa wuraren kwanan daliban da muhallin karatu sun dace da daliban da aka mayar daga Mussa.
Bam ya hallaka yan ta'adda a Borno
A baya, kun ji cewa bam ya tashi da wasu manyan 'yan ta'adda na kungiyar ISWAP kafin lokacin da suka shirya tashinsa domin cutar da bayin Allah a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da 'yan ta'addan ke kokarin hada bam a yankin Jubilaram, daya daga cikin yankunan da ake ganin ayyukan miyagun mutanen a jihar.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan sojojin Najeriya da na Amurka sun kashe Abu Mainok, wani babban kwamandan ISIS a tafkin Chadi a kokarin da dakaru ke yi na fatattakar yan ta'adda a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


