Zaben ADC: Atiku Abubakar Ya Shiga Gaba, Ya Samu Gagarumar Nasara a Jihohi 5
- Jam'iyyar ADC ta fara sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa da ta gudanar a ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026
- Rahotanni sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shiga gaban sauran yan takara a jihohi biyar da aka sanar
- Masu sharhi kan harkokin siyasa siyasa sun ce sakamakon zaɓen ADC zai yi tasiri yunkurin haɗakar jam’iyyun adawa da ke neman ƙalubalantar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya fara samun gagarumar nasara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar adawa ta ADC.
A sakamakon da ke fitowa daga jihohi, Atiku ya yi nasara a jihohi biyar yayin da ake ci gaba da kidaya kuri'u, wanda zai tantance dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027.

Source: Twitter
Atiku Abubakar ya shiga gaba a zaben ADC
Jaridar Punch ta ce zaɓen ya ja hankalin ‘yan siyasa da masu bibiyar harkokin ƙasa, inda Atiku ke fafatawa da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da masani tattalin arziƙi, Mohammed Hayatu-Deen.
Ko da yake ADC ba ta sanar da sakamakon ƙarshe daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya ba, sakamakon da aka samu daga wasu jihohi ya nuna Atiku na kan gaba da rinjayen ƙuri’u.
Jihohi 5 da Atiku ya yi nasara a ADC
Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya yi nasara a jihohin Gombe, Abia, Ebonyi, Sokoto da Zamfara, lamarin da ke ƙara nuna yiwuwar samun tikitin takarar shugaban ƙasa.
A jihar Gombe, sakamakon da jami’in tattara sakamako, David Agbu, ya sanar ya nuna cewa Atiku ya samu ƙuri’u 139,334. Amaechi ya zo na biyu da ƙuri’u 1,150, yayin da Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 464.

Kara karanta wannan
Nnaji: Ministan da Tinubu ya kora saboda jabun takardu ya samu takarar gwamna a PDP
A jihar Abia kuma, Atiku ya samu nasara da ƙuri’u 25,153, inda Amaechi yana da mutum 18,339, yayin da Hayatu-Deen ya samu 3,264.
A Ebonyi, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sake samun nasara, ya tashi da ƙuri’u 15,300 yayin da Amaechi ya samu ƙuri’u 2,200, Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 200.
A jihar Sokoto kuwa, Atiku ya samu ƙuri’u 68,823, yayin da Amaechi ya samu 292, Hayatu-Deen kuma ya samu 319.
Haka kuma a Zamfara, Atiku ya samu ƙuri’u 60,500. Hayatu-Deen ya samu 436, yayin da Amaechi ya samu 191, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
Atiku, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓukan 2019 da 2023, na daga cikin fitattun jagororin adawa a Najeriya.
Masu sharhi kan siyasa sun ce sakamakon zaɓen ADC zai yi tasiri a yunkurin haɗakar jam’iyyun adawa da ke neman ƙalubalantar APC a zaɓen 2027.
An gargadi Atiku kan takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa malamin duba, wanda ya kafa kungiyar One Love Family, Satguru Maharaj Ji ya yi magana game da takarar Atiku Abubakar a zaben 2027.

Kara karanta wannan
NDC ta yi zargin wasu shugabanninta na karbar na goro domin tsayar da 'dan takara
Malamin ya gargadi tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kada ya yi takara a zaben shekarar 2027 da ake tunkara a kasar nan.
Ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar siyasa tsakanin Arewa da Kudu wadda ta tsara yadda ake musayar mulki domin tabbatar da daidaito a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
