Gwamna na Shirin Karambanin Murabus Ya Nemi Sanata a 2027

Gwamna na Shirin Karambanin Murabus Ya Nemi Sanata a 2027

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya bayyana cewa ya amsa kiran jama'arsa domin neman kujerar Sanata a babban zaben 2027
  • An bayyana cewa akwai alamun Uzodimma zai yi murabus ya nemi Sanata kasancewar ba a 2027 wa'adin shi na gwamna zai kare ba
  • An fara rade-radin cewa bukatar neman kujerar shugaban majalisar dattawa ne ke shirin sa gwamnan Imo neman murabus daga mukaminsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Imo ta Yamma a shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC mai mulki ke cigaba da tantance masu neman takara da suka riga suka saye fom.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma
Gwamna Hope Uzodimma a wajen taron APC. Hoto: Hope Uzodimma
Source: Facebook

Uzodimma, wanda ke wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Uzodimma zai nemi Sanata

A sakon da ya wallafa, Hope Uzodimma ya bayyana cewa mutane ne suka bukaci ya fito takarar Sanata domin ya wakilce su a zaben 2027.

“Al’ummata na mazabar Imo ta Yamma sun sake kira na domin yi masu hidima, kuma na amsa wannan kira mai daraja cikin tawali’u, tsantsar niyya da cikakken jajircewa wajen ci gaban al’ummarmu baki ɗaya,”

In ji shi.

Gwamnan ya ce ya gabatar da kansa gaban shugabannin jam’iyyarsa ta APC da kuma kwamitin tantance ’yan takarar zaɓen fidda-gwani na majalisar dokoki ta ƙasa.

Tun kafin zama gwamna, Uzodimma ya wakilci mazabar a majalisar dattawa daga ranar 6 ga Yuni, 2011 zuwa 9 ga Yuni, 2019.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma
Lokacin da APC ta tantance gwamnan Imo a Abuja. Hoto: Hope Uzodimma
Source: Facebook

Kujerar gwamna da majalisar dattawa

Shigar Uzodimma cikin takarar majalisar dattawa na zuwa ne shekara biyu da watanni huɗu bayan rantsar da shi karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Imo.

Ya zama gwamnan Imo ne a shekarar 2020 bayan Kotun Koli ta soke zaɓen tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha tare da ayyana Uzodimma, wanda ya zo na huɗu a zaɓen 2019, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Masu neman takara 6 sun hakura, an bar wa Shekarau tikitin sanatan Kano ta Tsakiya

Wa’adinsa na biyu zai ƙare a watan Janairun 2028 kuma ana sa ran za a rantsar da sabuwar majalisar dattawa a watan Yunin 2027.

Batun murabus din gwamnan Imo

Premium Times ta rahoto cewa majiyoyi da dama sun yi iƙirarin cewa Uzodimma ya kammala shirye-shiryen yin murabus daga muƙaminsa na gwamna domin neman takarar majalisar dattawa.

Majiyoyin sun ce gwamnan ya cimma yarjejeniya da mataimakiyarsa, Chinyere Ekomaru domin ta yi murabus da kanta, wanda hakan zai buɗe hanya ga naɗa sabon mataimakin gwamna.

Uzodimma na fatan zama Sanata

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnonin APC sun fara nuna alamun goyon shugabansu, Hope Uzodimma ya zama Sanata a 2027.

An bayyana cewa hakan na cikin fatan gwamnonin jam'iyyar na ganin cewa gwamnan ya zama shugaban majalisar dattawa bayan zaben 2027.

Duk da cewa ya bayyana cewa bai san da shirin da wasu gwamnoni suka fara ta bayan fage ba, gwamnan ya ce yana maraba da fatan alherin da ake masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng