APC Ta Hana 'Yan Siyasa 47 Shiga Takarar Sanata, Ta Saki Cikakken Jerin Sunayen

APC Ta Hana 'Yan Siyasa 47 Shiga Takarar Sanata, Ta Saki Cikakken Jerin Sunayen

Abuja - Jam’iyya mai mulki ta APC ta fitar da jerin sunayen masu neman takarar kujerar sanata guda 47 da ba su samu amincewar shiga zaben fitar da gwani ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Felix Morka, ya sanya wa hannu ranar Litinin.

Jam'iyyar APC ta hana mutane 47 shiga takarar zaben fitar da gwani na kujerar sanata.
Tutar jam'iyyar APC a wani babban taron jam'iyyar da aka gudanar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

APC ta hana mutane 47 neman takara

An wallafa sanarwar da Felix Morka ya fitar ne a shafin jam'iyyar na X, wacce ke dauke da hotunan jadawalin sunayen masu neman takarar da aka hana shiga zaben fitar da gwani.

A cewar sanarwar, kwamitocin tantance ‘yan takara na jam’iyyar ne suka gudanar da aikin bisa tanade-tanaden da APC ta shimfida domin tantance masu neman tikiti.

Daya daga cikin manyan sunayen da suka fito a cikin jerin wadanda aka hana shiga zaben fitar da gwanin shi ne tsohon sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Ben Murray-Bruce.

Kara karanta wannan

Jerin masu neman takarar majalisar tarayya da APC ta yi watsi da su a wurin tantancewa

APC ba ta fadi dalilin matakin ba

Haka kuma, Benson Agadaga, wanda shi ma ya nemi tikitin Bayelsa ta Gabas, bai samu tsallake tantancewar ba.

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa APC ba ta bayyana takamaiman dalilan da suka sa aka hana wadannan ‘yan takara shiga zaben ba.

Jihar Zamfara ce ta fi yawan ‘yan takarar da suka fadi tantancewar, inda mutum hudu daga mazabar Rivers ta Yamma suka rasa damar shiga zaben fidda gwani.

Jerin mutum 47 da APC ta hana takara

Ga cikakken jerin sunayen mutum 47 da jam'iyyar APC ta hana shiga takara a zaben fitar da gwani:

Adamawa - 2

  • Hamish Idris — Adamawa ta Arewa
  • Abdurman Kwacham — Adamawa ta Arewa

Anambra - 1

  • Chimzobam Kingsley Nnalue — Anambra ta Arewa

Bayelsa - 3

  • Donald Daunemigita — Bayelsa ta Yamma
  • Ben Murray-Bruce — Bayelsa ta Gabas
  • Benson S. Agadaga — Bayelsa ta Gabas

Cross River - 2

  • Daniel Effiong Asuquo — Cross River ta Kudu
  • Oden Ibiang O Ewa — Cross River ta Tsakiya

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a zaben fitar da gwani na APC, an tarwatsa masu kada kuri'a

Delta - 1

  • Marian Nnamaka Ogoha-Ali — Delta ta Arewa

Abuja (FCT) - 2

  • Usman J. Wowo
  • Abubakar Umar Abdullahi

Jigawa - 1

  • Adam Mouktar Mohammed — Jigawa ta Kudu maso Yamma

Kebbi - 1

  • Garba Musa Mai Doki — Kebbi ta Kudu

Kwara - 4

  • Kollo B. Jiya — Kwara ta Arewa
  • Olutola John Onijala — Kwara ta Kudu
  • Awolola Muritala — Kwara ta Kudu
  • Adeleke Emmanuel Gbenga — Kwara ta Kudu

Nasarawa - 4

  • Abdullahi Tanko Zubairu — Nasarawa ta Arewa
  • Usman Muhammed Elegu — Nasarawa ta Kudu
  • Yusuf Moh’d Agabi — Nasarawa ta Kudu
  • Ari Ali Muhammed — Nasarawa ta Kudu

Neja - 3

  • Muhammed Rabiu Sadiq — Neja ta Kudu
  • Muhammed Bello A. — Neja ta Kudu
  • Bello Bawa Bwari — Neja ta Kudu

Oyo - 6

  • Ademola Wasiu Alli — Oyo ta Tsakiya
  • Ajimobi Wasiu Adegboyega — Oyo ta Arewa
  • Kolapoboye Kola Daisi — Oyo ta Kudu
  • Faozey Oladotun Nurudeen — Oyo ta Tsakiya
  • Hameed Afeez Repete — Oyo ta Tsakiya
  • Akinremi Alade Bolaji — Oyo ta Kudu

Kara karanta wannan

Sulhu ko kato bayan kato: Jam'iyyar APC ta kaddamar da fara zaben fitar da gwani

Plateau - 3

  • Gyang Yaya Zi San — Plateau ta Arewa
  • Napoleon Binkap Bah — Plateau ta Kudu
  • Usman Ephraim Gar — Plateau ta Tsakiya
Sanata Ben Murray-Bruce ya shiga jerin wadanda APC ta hana takara a 2027
Sanata Ben Murray-Bruce da tutar jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg, @benmurraybruce
Source: Twitter

Rivers - 5

  • Oyukaye Flag Amachree — Rivers ta Yamma
  • Tamunobaabo Wemike Danagogo — Rivers ta Yamma
  • Jack-Rich Tein T.S — Rivers ta Yamma
  • Banigo Ipalibo — Rivers ta Yamma
  • Barry Balera Mwara — Rivers ta Kudu maso Gabas

Taraba - 1

  • Bello Abudullahi Bodejo — Taraba ta Tsakiya

Yobe - 1

  • Hassan H. Kafayos — Yobe ta Arewa

Zamfara - 7

  • Sanusi Ibrahim Garachi — Zamfara ta Tsakiya
  • Aliyu Abubakar — Zamfara ta Tsakiya
  • Muhammad Bashir Maru — Zamfara ta Tsakiya
  • Hassan Muhammad Gusau — Zamfara ta Tsakiya
  • Abubakar H. Moriiki — Zamfara ta Arewa
  • Bilyaminu Yusuf — Zamfara ta Arewa
  • Isyaka Ajiya Anka — Zamfara ta Yamma

APC ta yarda Yahaya Bello ya nemi takara

A wani labari, mun ruwaito cewa, Yahaya Bello da Sanata Sunday Karimi na cikin ’yan takarar da APC ta amince su fafata a zaɓen fitar da gwani na sanatoci a Kogi.

Kara karanta wannan

2027: Masu neman takara sun cika sakatariyar APC da gidan shugaban jam'iyya

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, zai kara da Momoh Yusuf Obaro da Ibrahim Yakubu Adoke domin neman tikitin APC na Kogi ta Tsakiya.

Jam’iyyar PDP ta fitar da ’yan takarar majalisar wakilai ta hanyar maslaha a wasu mazaɓu, yayin da tsofaffin ’yan majalisa suka samu tikiti a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com