Tirkashi: Yadda Shugaban Hukumar Bogi Ta PFIPC Ya Damfari Dan Kasuwa N400m
- Gbenga Collins ya ce ya ba Adeniyi Adeyemi N400m domin a saukaka ba kamfaninsa kwangilar gyara da samar da kayan daki
- Ya ce ya yarda da PFIPC a matsayin hukumar gwamnati saboda Adeyemi na aiki daga sakatariyar tarayya a Abuja
- Collins ya ce daga baya lauyansa ya sanar da shi cewa an damfare shi, bayan an kasa fara biyan kudin kwangilar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gbenga Collins, daraktan gudanarwa na Divine Dopacy Nigeria Limited, ya ce ya ba Adeniyi Adeyemi N400m.
Ya ce ya ba Adeyemi kudin ne domin a saukaka wa kamfaninsa samun kwangilar gyara da samar da kayan daki a wani gida da Adeyemi ya ce shi ne mazauninsa na hukuma.

Source: Facebook
The Cable ta ce Collins ya bayyana haka ne ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026 lokacin da ya gurfana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye hukumar PFIPC.
Kwamitin yana kuma binciken yadda aka ware N1.3 biliyan ga hukumar a dokar kasafin kudin 2026.
Dalilin da ya sa Collins ya yarda
Collins ya ce ya dauki PFIPC a matsayin halastacciyar hukumar gwamnatin tarayya saboda Adeyemi na aiki daga wani ofishi da ke sakatariyar tarayya a Abuja.
Ya ce Adeyemi yana amfani da motocin hukuma masu lambobin gwamnati, sannan jami’an tsaro suna tare da shi.
Dan kasuwar ya ce ya fara haduwa da Adeyemi a watan Disamban 2024, lokacin da ya gabatar da kansa a matsayin babban daraktan PFIPC da kuma PEAC.
Collins ya shaida wa ‘yan majalisar cewa daga baya Adeyemi ya sanar da shi shirinsa na gyara mazauninsa na hukuma, tare da gayyatar kamfaninsa domin gudanar da aikin.
Yadda aka ba kamfanin kwangilar
Collins ya ce Adeyemi da kansa ya kai shi wajen domin duba gidan, tare da wasu ma’aikata da jami’an tsaro.
Ya kara da cewa a watan Afirilun 2025, Adeyemi ya ba shi takardar ba da kwangila, bayanin ayyukan da za a gudanar da kuma yarjejeniyar gyaran gidan.
Dan kasuwar ya ce daga baya Adeyemi ya bukaci ya bayar da N400 miliyan a matsayin tabbacin cewa kamfaninsa na da karfin kudi, da kuma domin saukaka fara aikin kwangilar.
“Dole na biya N400 miliyan domin a saukaka aikin, tare da nuna cewa ina da karfin da zan iya gudanar da aikin.” In ji shi
Collins ya ce ya tara kudin ne daga wasu abokan hulda da suka yarda da shi saboda ya ziyarci ofishin Adeyemi da kansa, kuma ya yi imanin yana mu’amala da halastacciyar hukumar gwamnati.
Yadda aka biya N400 miliyan
Ya ce an biya kudin ne kashi biyar tsakanin watan Mayu da Yulin 2025, ta wasu asusun World Entrepreneurs Limited da Sunshine Confectionery and Catering Services.
Collins ya ce duk da alkawuran da aka rika ba shi, ba a taba fitar da kudin fara aikin ba, jaridar Leadership ta kawo labarin.
A cewarsa, an fara yi masa alkawarin cewa za a fara biyan kudin a watan Agustan 2025, daga baya kuma aka ce watan Nuwamban 2025.
“Lauyana ne mutum na farko da ya gaya min cewa an damfare ni.” Inji shi
Ya kara da cewa daga baya an shigar da kara gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki (EFCC).

Source: Facebook
Collins ya musanta bayar da cin hanci
Ko da yake Collins ya amince cewa bai bi dokar sayen kaya da bayar da kwangilolin gwamnati ba, ya musanta cewa ya bayar da kudin a matsayin cin hanci.
Ya ce ya yi imanin cewa bayar da N400 miliyan sharadi ne da zai saukaka wa kamfaninsa samun kwangilar.
Dan kasuwar ya roki kwamitin majalisar wakilai ya taimaka wajen kwato masa kudin daga Adeyemi.
Adeniyi ya yi fallasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya musanta zargin cewa shi kaɗai ya ƙirƙiri hukumar da ake takaddama a kanta.
Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya sun gudanar da ayyuka, sun amince ko kuma sun yi hulɗa da hukumar.
Asali: Legit.ng


