Gwamna Fintiri Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, an Sauya Kwamoshinoni

Gwamna Fintiri Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, an Sauya Kwamoshinoni

  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi garambawul a gwamnatinsa, inda ya sauya wurin aiki ga wasu kwamishinoni
  • Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci kwamishinonin da abin ya shafa da su ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban Adamawa
  • A cewar sanarwar da aka fitar game da garambawul da Gwamna Fintiri ya yi, sauye-sauyen za su fara aiki ne nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Gwamnan Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, CON, ya sake gudanar da garambawul a cikin majalisar zartarwar jihar.

Gwamna Fintiri ya sauyawa wasu kwamoshinoni ma'aikatun da za su ci gaba da jagoranta a jihar Adamawa.

Gwamna Fintiri ya yi garambawul a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: @GovernorAUF
Source: Twitter

Babban sakataren yada labaran gwamnan Adamawa, Humwashi Wonosiku, ya fitar wadda hadimin Fintiri ya sanya a shafinsa na X a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Wadanne kwamishinoni sauyin ya shafa?

Sanarwar ta bayyana cewa wadannan sauye-sauyen da Gwamna Fintiri ya yi, za su fara aiki ne nan take.

Mambobin majalisar da abin ya shafa sun haɗa da Mista Joab Sahma, kwamishinan filaye da Safiyo, wanda aka tura zuwa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu.

Shi kuwa Dr. John Ishaya Dabari ya tashi ne daga ma’aikatar kasuwanci zuwa ta filaye da safiyo domin ci gaba da jagorantar ta.

Meyasa Gwamna Fintiri ya yi sauyin?

A cikin sanarwar Gwamna Fintiri ya bayyana cewa:

“Wannan sauyin wurin aiki an yi shi ne da nufin samar da sabon kuzari da karfin gwiwa wajen gudanar da ayyuka, wanda shi ne maƙasudin gwamnatinmu."

Ya buƙaci kwamishinonin biyu da su ci gaba da bayar da gudunmawarsu yadda ya kamata a sababbin muƙaman nasu.

Gwamnan ya yi kira gare su da su rungumi wannan aiki da sabon jajircewa tare da tafiya kafada da kafada da manufofin gwamnati ta hanyar aiwatar da kyawawan tsare-tsare da shirye-shirye waɗanda za su inganta rayuwar al’ummar jihar Adamawa kai-tsaye.

Kara karanta wannan

Abba ya sulhunta Barau da Gwarzo, an samu wanda ya hakura da takarar sanata a 2027

Gwamna Fintiri ya yi garambawul

Tun da farko Gwamna Fintiri ya yi wani garambawul, inda kwamishinan bunƙasa makamashi, Mohammed Chubado, aka tura shi ma’aikatar lafiya, yayin da kwamishinan bunƙasa kiwon dabbobi, Sali Idris, aka tura shi kula da ma’aikatar noma.

Gwamna Fintiri ya sauyawa wasu kwamishinoni wurin aiki
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Haka zalika, kwamishinan ayyuka na musamman, Usman Lamurde, zai jagoranci ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi.

An kuma rantsar da Leder Leneke a matsayin sabon kwamishinan yaɗa labarai da dabaru, biyo bayan tantance shi da majalisar dokokin jihar Adamawa ta yi.

Leder Leneke ya karɓi ragamar jagoranci ne daga hannun James Iliya, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa domin neman takarar zaɓe.

Yaron Atiku ya bar gwamnatin Fintiri

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaron tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishina a gwamnatin Adamawa.

Adamu Atiku Abubakar ya sanar da murabus daga mukamin kwamishinan ayyuka da ci gaban makamashi na jihar Adamawa.

Tsohon kwamishinan ya mika sakon godiya ta musamman ga gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, bisa yadda ya nuna masa amincewa da kuma ba shi damar taka rawar gani a gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng