Akwai Matsala: An Yi Kutse a Daya daga cikin Manyan Bankunan da Ake Amfani da Su a Najeriya

Akwai Matsala: An Yi Kutse a Daya daga cikin Manyan Bankunan da Ake Amfani da Su a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa wasu masu kutsen yanar gizo sun kai hari kan bayanan Zenith Bank, daya daga manyan bankunan Najeriya
  • Bankin ya ce masu kutsen sun samu bayanan wasu abokan hulda da ke da asusu, wanda suka hada da imel da lambobin waya
  • Zenith Bank ya tabbatar da cewa ayyukan banki da hanyoyin sadarwa na zamani suna cikin aminci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Zenith Bank, daya daga cikin manyan cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya, ya tabbatar da cewa masu kutse sun yi kutse a rumbun ajiyar bayanan abokan huldarsa.

Rahotanni sun nuna cewa masu kutsen sun dauki bayanan wasu kwastomin bankin, wanda ya kunshi lambobin waya da adireshin imel.

Bankin Zenith.
Daya daga cikin rassan bankin Zenith da ke aiki a Najeriya Hoto: Zenith Bank Plc
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta rahoto cewa bankin ya bayyana hakan ne a cikin sakon imel da ya aika wa kwastomominsa ranar Talata da ta gabata.

Kara karanta wannan

Wike zai hana sana'ar acaba da masu adaidaita sahu aiki a birnin Abuja

Bankin Zenith ya ce wannna kutse da aka masa wani bangare ne na wani babban hari na yanar gizo da ake kai wa kungiyoyi da cibiyoyin hada hadr kudi a sassa daban-daban na duniya.

Abin da masu kutsen suka dauka

Zenith Bank ya ce masu kutse sun samu damar shiga wasu bayanan kwastomomi kadan, ciki har da adireshin imel da lambobin waya.

Sai dai bankin ya jaddada cewa lamarin bai shafi manyan bayanan sirri ko ayyukansa ba, yana mai cewa hanyoyin hada-hadar kudi da na’urorin sadarwa na zamani suna ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Bankin Zenith ya fara bincike

Bankin ya ce bayan gano matsalar, nan take ya kunna tsare-tsaren mayar da martani ga matsalar tsaro tare da kara amfani da matakan kare bayanai.

Ya ce:

“A matsayin matakin kariya, muna kira ga kwastomominmu da su ci gaba da taka tsantsan kan sakonnin bogi ta imel, sakonnin waya ko kira, sannan kada su taba bayyana lambobin sirri na PIN, One-Time Password (OTP) ko wasu bayanan tsaro ga kowa.”

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

Zenith Bank ya bayyana cewa yana ci gaba da daukar matakan kare bayanan kwastomomi, tare da gode musu bisa amincewar da suke ci gaba da nuna masa.

CBN ya yi gargadi kan hare-haren yanar gizo

Harin na baya-bayan nan ya kuma zo ne watanni kadan bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi jama’a kan yunkurin masu kutse na samun damar shiga asusun mutane.

CBN ya ce masu aikata laifukan yanar gizo na aika sakonnin bogi da imel da suke nuna kamar sun fito daga bankin domin yaudarar ‘yan Najeriya.

Ya ce sakonnin na bogi kan kunshi hanyoyin sadarwa da ke neman mutane su danna wasu shafuka masu hadari, tare da yada bayanan karya kan shugabancin bankin, lasisi da manufofinsa.

CBN ya soke lasisin bankuna 46

Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankunan microfinance 46 daga ranar 1 ga Yuli, 2026 bisa gazawar cika ƙa’idojin aiki.

CBN ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bisa ikon da doka ta ba shi ƙarƙashin dokar bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade (BOFIA) ta 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262