Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Sabon Tsarin Karatun Allo, Ta Haramta wa Almajirai Bara

Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Sabon Tsarin Karatun Allo, Ta Haramta wa Almajirai Bara

  • Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin karatun allo, inda ta haramta tura yara bara tare da kafa hukunci ga cibiyoyin da suka karya doka
  • Sabon tsarin ya haɗa da koyar da karatu, lissafi, fasahar zamani da sana'o'i, ba tare da sauya tsarin karatun Alƙur'ani da addini ba
  • Haka kuma, an wajabta wa dukkan makarantun almajirai yin rajista, tattara bayanan ɗalibai da ba su takardar shaidar kammala karatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin inganta ilimin almajirai, inda ta haramta wa cibiyoyin karatun almajirai tura yara bara a tituna.

Sabon tsarin, wanda Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da shi, ya kuma wajabta koyar da karatu, lissafi, fasahar zamani da koyon sana'o'i a makarantun almajirai.

Gwamnati ta kawo sabon tsarin karatun allo
Almajirai na daukar karatu daga malamansu a wata makarantar allo. Hoto: Kristin Palitza/picture alliance via Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnati ta haramta bara ga almajirai

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Haka kuma, gwamnatin ta umurci dukkan cibiyoyin karatun almajirai da su yi rajista, su tattara bayanan ɗalibai da na halittarsu (biometric), tare da ba wa waɗanda suka kammala karatu takardar shaida da gwamnati za ta amince da ita, in ji rahoton Punch.

A cikin kundin sabon tsarin, gwamnatin ta bayyana cewa ba za a ƙara yarda da tura almajirai bara ko yin ayyukan wahala domin neman kuɗi ba.

Ta gargaɗi cewa duk wata cibiyar da aka yi wa rajista da aka kama tana tura yara bara za ta fuskanci hukunci, har da yiwuwar rufe makarantar.

Gwamnatin ta ce ɗaya daga cikin manyan manufofin tsarin shi ne kawo ƙarshen bara, cin zarafi da nuna wariya da ake dangantawa da tsarin almajiranci, tare da kare haƙƙin yara.

Za a koyar da karatu da sana'o'i

Sabon tsarin ya tanadi cewa za a haɗa darussan karatu da lissafi cikin tsarin koyarwa a dukkan makarantun almajirai a faɗin ƙasar nan.

Haka kuma, za a koyar da fasahar zamani, ilimin sana'o'i, harshen Larabci, ilimin zamantakewa da dabarun rayuwa domin bai wa ɗalibai ƙwarewar da za ta taimaka musu a nan gaba.

Gwamnatin ta ce ɗalibai za su sami damar koyon sana'ar da suka zaɓa ko wadda iyayensu ko masu kula da su suka amince da ita domin inganta rayuwarsu bayan sun kammala karatu.

Kara karanta wannan

Kano za ta karbi manyan baki, akwai babban taro a kan miyagun kwayoyi

Gwamnatin tarayya ta ce ba ta kawo tsarin don rutse makarantun allo ba sai don zamanantar da harkar almajiranci
Ministan ilimin Najeriya, Dr. Tunji Alausa yana jawabi a wani taro. Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Sabbin ƙa'idoji ga makarantun allo

Sabon tsarin ya kuma wajabta wa dukkan cibiyoyin karatun almajirai yin rajista a hukumomin jihohi ko ƙananan hukumomi, tare da adana cikakken bayanin ɗalibai da na halittarsu.

An kuma shimfiɗa sabbin ƙa'idoji kan lafiya da walwalar ɗalibai, ciki har da gwajin lafiya kafin karɓar su makaranta, samar da tsaftataccen ruwa, bandaki, akwatin agajin farko da wuraren karatu daban-daban ga maza da mata.

Gwamnatin ta jaddada cewa manufar sabon tsarin ba rushe tsarin almajiranci ba ce, illa gyara shi domin kare lafiyar yara, inganta rayuwarsu da ba su damar samun ilimi da ƙwarewar da za su taimaka musu wajen dogaro da kai.

Gwamnati ta fito da shiri ga almajiran Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar Almajirai ta sanar da shiri domin bayar da horo na musamman na wata tara ga almajirai masu karatu a tsangaya.

Shirin, wanda aka tsara tsawon watanni tara, zai bai wa almajiran tsangaya damar samun ilimi da sana’o’i, wanda zai basu damar dogaro da kansu a rayuwa.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa guraben karatun ba su da yawa, don haka sai wanda ya cika sharuddan da aka gindiya ne ake maraba da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com