Dan APC Ya Sha Wahala, Yana Neman Jam’iyyar Ta Saka Masa kan Bautar da Ya Yi
- Wani ɗan jam'iyyar APC daga Delta, Daniel Solomon, ya bayyana dawainiyar da ya yi gare ta amma babu sakamako har yanzu
- Solomon ya ce ya bai wa gwamnatin APC wa'adin sa'o'i 72 ta karɓi yaransa, yana mai gargadin wani mummunan abu na iya faruwa
- Ya ce ya sayar da kadarorinsa domin ya yi wa 'yan siyasar APC kamfen a zaɓen 2023, amma har yanzu bai samu wani tallafi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Wani ɗan Najeriya daga Delta mai suna Daniel Solomon ya ba jam'iyyar wa'adin awanni 72 saboda wahalar da ya sha mata.
Mutumin ya roƙi jam'iyyar APC ta dauki dawainiyar kula da 'ya'yansa shida, yana mai cewa tsananin matsin tattalin arziki ya sa ba zai iya ci gaba da kula da su ba.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya tubure kan dokar gwamnatin Tinubu na hana wa'azi, ya sha alwashi

Source: Twitter
Solomon ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta da Tribune ta samu inda ya ce shi ɗan jam'iyyar APC ne a Delta.
Mutumin ya kuma roƙi jama'a su yaɗa bidiyon domin ya isa ga hukumomin gwamnati domin su yi abin da ya dace.
Ya ce ya bai wa gwamnatin APC wa'adin sa'o'i 72 ta karɓi 'ya'yansa shida, yana mai gargadin cewa idan ba a kai musu ɗauki cikin wannan lokaci ba, yana tsoron ɗaukar wani mataki mai muni.
Solomon ya kuma zargi wani sanatan APC mai ci daga Delta da haddasa matsalolin da suka jefa shi cikin talauci.
Ya ce ya rasa motoci shida, gidansa, aurensa da kuma damar ci gaba da karatun lauya.
Ya yi kira ga gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da sauran shugabannin siyasa a jihar da su tuna cewa ya mara musu baya tare da yi musu kamfen a lokacin zaɓen shekarar 2023.
A cewarsa, ya sayar da kadarorinsa domin tallafa wa kamfen ɗinsu, amma duk da irin sadaukarwar da ya yi, bai samu wani tallafi daga gare su ba.
Ya ce ya ga gwamnati tana tallafa wa wasu ta shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki, saboda haka ya roƙi a kawo masa agajin gaggawa, yana mai cewa matsin rayuwa da takaici sun yi masa yawa.
A wani ɓangare na saƙonsa, Solomon ya roƙi gwamnati ta karɓi kula da 'ya'yansa cikin gaggawa kafin lamarin ya ƙara taɓarɓarewa, yana mai bayyana cewa ba ya son halin da yake ciki ya kai ga wani mummunan sakamako.
Masoyin Tinubu ya hakura da tallata shi
A wani labarin, an ji cewa wani fitaccen masoyin Bola Tinubu a Kebbi, Adam Fakai, ya dakatar da tallata ayyukan gwamnatin tarayya bayan fiye da shekara biyu yana yi da kuɗinsa.
Adam Fakai ya ce bai samu wata kulawa ko goyon baya daga shugabannin APC a Kebbi ko matakin tarayya ba duk da ƙoƙarinsa wajen yaɗa ayyukan Tinubu.
Amma ya ce hakan ba ya na nufin ya daina goyon bayan Tinubu ba, illa dai dakatar da aikin tallata gwamnati saboda halin ko in kula da aka nuna masa.
Asali: Legit.ng
