An Kashe na Kashewa da Sojojin Israila Suka Sha Wuta a Lebanon
- Rahotanni sun nuna cewa sojojin Isra’ila sun mutu, yayin da wasu suka jikkata bayan fashewar wani bam a wani gini da aka shirya masa tarko a kudancin Lebanon
- An ce sojojin biyu mambobi ne na runduna ta 55, kuma sun mutu ne bayan fashewar bam din a cikin wani gini da sojojin Isra’ila suka dade suna iko da shi
- Lamarin ya faru ne bayan wasu sojojin Isra’ila sun jikkata sakamakon fashewar nakiya a garin Majdal Zoun da ke Kudancin Lebanon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kudancin Lebanon - Sojojin Isra’ila biyu sun mutu, yayin da wasu bakwai suka jikkata ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026.
Sojojin na Israila sun sheka barzahu ne bayan fashewar wani bam a cikin wani gini da aka shirya masa tarko a Kudancin kasar Lebanon.

Source: Getty Images
Rahoton tashar Roya News ya nuna cewa sojojin biyu mambobi ne na runduna ta 55, kuma sun mutu ne lokacin da bam din ya tashi a cikin ginin.
An ce sojojin Isra’ila sun dade suna iko da ginin da lamarin ya faru a cikinsa, yayin da sauran sojoji bakwai da ke cikin ginin suka jikkata sakamakon fashewar.
Nakiya ta jikkata sojojin Israila
Tun da farko a ranar Laraba, kafafen yada labaran Israila sun ruwaito cewa wasu sojojin Isra’ila sun jikkata bayan fashewar wata nakiya a garin Majdal Zoun da ke Kudancin Lebanon.
Rahoton tashar Aljazeera ya ce an kwashe sojojin da suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa ta hanyar jiragen saman rundunar sojin Isra’ila.
An jikkata babban sojan Isra’ila
Sababbin abubuwan da suka faru sun biyo bayan wani lamari da ya faru ranar Asabar da ta gabata, lokacin da wani hafsan sojin Isra’ila ya jikkata a yayin arangama da mayakan Hezbollah a yankin Ali al-Taher da ke kudancin Lebanon.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da gudanar da ayyuka a Lebanon tun ranar 2 ga watan Maris, 2026, yayin da hukumomin Lebanon suka ce dubban mutane sun mutu ko suka jikkata sakamakon rikicin da ke ci gaba da tsananta.
Har yanzu sojojin Isra’ila na ci gaba da rike iko da wasu yankuna a kudancin Lebanon, ciki har da wuraren da suka shafe shekaru masu yawa suna rike da kuma wasu da suka kwace a yayin sababbin arangama.
Haka kuma, sojojin Isra’ila sun kara fadada kasancewarsu zuwa wasu yankuna da ke zurfin kasar Lebanon a yayin farmakin da suke gudanarwa.

Source: Getty Images
Lokacin ficewar sojojin Israila daga Gaza
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Board of Peace karkashin jagorancin Amurka ta ce janyewar sojojin Isra’ila daga Zirin Gaza ba za ta faru ba sai bayan an kammala kwace makaman Hamas.
Hukumar ta bayyana hakan ne bayan ganawar da daraktanta, Nickolay Mladenov, ya yi da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
Tun bayan yarjejeniyar tsagaita wutar, Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 1,200, ciki har da fiye da 36 bayan sanar da yarjejeniyar kwace makaman.
Asali: Legit.ng

