APC Ta Jaddada Yadda Tsarin Zaben Fitar da Gwani na Shugaban Kasa Zai Kasance
- Jam’iyyar APC ta yi magana game da tsarin da za ta yi amfani da shi a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na 2027
- Zaben fitar da gwani zai gudana a dukkan mazabu 8,809 na Najeriya, sannan a tattara sakamako daga matakin mazaba zuwa jiha kafin zuwa Abuja
- An kafa kwamitocin gudanarwa da na daukaka kara, tare da manyan shugabanni da tsofaffin gwamnoni domin kula da sahihancin zaben fidda gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta amince da amfani da tsarin zaben fitar da gwani kai tsaye domin zaben dan takarar shugaban kasa na shekarar 2027.
Wannan mataki zai bai wa dukkan mambobin jam’iyyar APC da aka yi rajista a fadin Najeriya damar kada kuri’a wajen zaben wanda zai wakilci jam’iyyar.

Source: Twitter
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na kasa, Felix Morka ya fitar, tare da cikakken tsarin gudanar da zaben fidda gwani, cewar Premium Times.
Tsarin da APC a zaben fitar da gwani
Sanarwar ta ce Kwamitin Zartarwa na Kasa (NWC) ya amince da matakan gudanar da zaben bisa kundin tsarin jam’iyya da dokar zabe ta kasa.
A tsarin, za a gudanar da zaben fitar da gwani a lokaci guda a dukkan mazabu 8,809 da ke fadin Najeriya.
Dukkan mambobin APC da aka yi rajista za su samu damar kada kuri’a ga duk dan takarar da suke so.
A halin yanzu, manyan ‘yan takara biyu ne ke neman tikitin APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Stanley Osifo daga Jihar Edo.
Sakamakon zabe zai fara tattaruwa daga mazabu zuwa kananan hukumomi, sannan zuwa jihohi kafin a tura zuwa Abuja.

Kara karanta wannan
Atiku ko Amaechi?: ADC ta sanya ranar da za ta tsayar da ɗan takarar shugaban kasa

Source: Twitter
Wadanda ke cikin kwamitin zaɓen fitar da gwani
An nada tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim a matsayin shugaban kwamitin zaben fidda gwani na shugaban kasa.
Sauran mambobi sun hada da Ken Nnamani, Victor Ndoma-Egba, Yakubu Dogara, Idris Wada da Grace Titi Laoye-Ponle, tare da Sanusi Musa a matsayin sakatare.
Haka kuma an kafa kwamitin daukaka kara karkashin jagorancin Aminu Bello Masari domin duba korafe-korafe na zaben.
Jam’iyyar ta kuma nada gwamnoni da manyan jami’ai a matsayin masu daidaitawa a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
APC ta ce wannan tsari na nufin tabbatar da sahihin zabe cikin gaskiya da bin ka’idojin dimokuradiyya a cikin jam’iyya, cewar rahoton Punch.
Gwamnan Kebbi ya samu tikitin takara
An ji cewa jam'iyyar APC ta samu dan takarar da zai fafata a karkashin inuwarta a zaben gwamnan jihar Kebbi na shekarar 2027.
APC ta amince da Gwamna Nasir Idris a matsayin dan takararta domin ya nemi wa'adi na biyu a shekarar 2027 da ake tunkara.
Gwamna Nasir Idris ya nuna godiyarsa kan amincewar da aka nuna masa, ya sha alwashin ci gaba da yin ayyuka a jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng
