Rigima na Kara Zafi da Iran, An Sake '"Yunkurin Kashe" Shugaban Kasar Amurka

Rigima na Kara Zafi da Iran, An Sake '"Yunkurin Kashe" Shugaban Kasar Amurka

  • An kama wani mutumi mai suna, Jeanine John Taele dauke da bindiga a kusa da filin wasan golf na Shugaban Amurka, Donald Trump
  • Rahoto ya nuna cewa an kama mutumin ne yayin da Trump ke shirin kai ziyara wurin wasan a jihar California
  • An same shi da bindiga da harsasai haramtattu yayin da yake daukar hotuna da bidiyo a wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

California, US - Ana zargin an sake yunkurin kai hari kan shugaban Amurka, Donald Trump amma jami'an tsaro sun yi nasarar rusa shirin.

An fara wannan zargi ne bayan hukumomi a jihar California ta Amurka sun kama wani mutum da aka gani kusa da filin wasan golf mallakar Shugaba Donald Trump, dauke da makamai.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin tattaunawa dayan jarida a fadar Whitr House Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

An dakile yunkurin kai wa Trump hari

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mutanen gari sun sassara wata mata da adda har ta mutu a Bauchi

BBC News ta ruwaito cewa an kama mutumin dauke da bindiga gabanin ziyarar da Trump ke shirin kai wa wurin domin halartar taron tara kudin yakin neman zaben jam’iyyar Republican.

Jami’an bincike sun ce an kama Jeanine John Taele, mai shekaru 38, ne a filin wasan golf na Trump National Golf Course da ke Rancho Palos Verdes, inda aka same shi da bindiga da harsasai da ba a yarda da su ba.

A cewar Hukumar Sheriff ta Los Angeles, an ga mutumin yana yawo a filin wasan yana daukar hotuna da bidiyo, sannan yana nuna kamar yana bibiyar shirye-shiryen tsaro da ake yi.

An kama shi ne ranar Lahadi da rana. Trump ya kai ziyarar California domin halartar wani taron tara kudin jam’iyyar Republican da aka shirya gudanarwa a filin wasan golf din ranar Talata.

Ana sa ran za a gurfanar da mutumin a gaban kotun tarayya ranar Alhamis domin yiwuwar amsa tuhumar da ake yi masa.

Hukumar FBI ta yi martani

Patrick Grandy, mataimakin daraktan Hukumar FBI ta Los Angeles, ya ce:

“Babu damar yin kuskure, musamman saboda yunkurin da aka taba yi a baya kan rayuwar Shugaba Trump.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi yanayin da zai sa ya shiga daji ceto daliban da aka sace

A ranar Litinin, jami’an FBI da ke aiki tare da rundunar yaki da ta’addanci da kuma sashen manyan laifuka na Hukumar Sheriff ta Los Angeles sun kai samame gidansa da ke Downey.

A gidan nasa, an gano bindigar AR da aka yi mata gyare-gyaren da ba su dace da doka ba, kayan kariya na jiki, mujallun harsasai masu yawa da harsasai iri daban-daban.

Gulf.
Wurin wasannin Gulf mallakin shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu Ajensi
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya kai ziyara California

Wannnan dai na zuwa ne gabanin wata ziyarar da Trump ya kai California, wadda ba kasafai yake yi ba.

Fadar White House ta ce Trump zai gabatar da jawabi mai sukar Gwamnan California, Gavin Newsom, wanda ake ganin yana shirin neman takarar shugaban kasa a zaben 2028.

Trump zai kuma je Las Vegas ranar Laraba domin gabatar da wani jawabi a wani gidan caca, kamr yadda Sky News ta rahoto.

Trump ya tsira daga yunkurin kisa sau uku a shekarun baya. Bayan yunkurin baya-bayan nan, jami’an tsaronsa sun ce za su sake duba tsarin kare shugaban kasar.

Trump ya gargadi Iran kan bude Hormuz

A wani rahoton, an ji cewa Shugaba Donald Trump ya ce da yiwuwar Amurka ta cimma yarjejeniya da Iran kan sake buɗe mashigar Hormuz nan ba da jimawa ba.

Trump ya yi barazanar cewa za a kai wa Iran hari mai tsanani idan tattaunawar ta gaza samar da sakamako mai kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262